Malam Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a jiya Juma’a 17/07/2020 yayin da yake gabatar da jawabi a wajen gudanar da bikin tunawa da haihuwar Annabi Isah dan Maryam (AS), wanda Dandalin Matasan Harka Islamiyya dake karkashin jagorancin Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) na Da’irar Saminaka suka shirya da yammacin jiya a harabar makarantar Fudiyya ta cikin garin Unguwar Bawa dake karamar Hukumar Lere ta jahar Kaduna. Cikin jawabin malamin yake cewa: “Lokacin da Allah Ta’ala ya yi umarni ga Sayyida Maryam (AS) yayin da zata samu cikin haihuwar Annabi Isah (AS), sai ya yi mata umarni da kasancewarta a kebe a wani waje har zuwa lokacin da Allah samar da cikin Annabi Isah (AS) a tattare da ita. Lokacin da ta samu cikinsa tayi tafiya mai nisan gaske, tana tafe har zuwa wajen wani kututturen itace, wanda dama Allah Ta’ala a nan ya kudurta cewa zata haifi Annabi Isah (AS)”.
Malamin ya ce, “Allah Ta’ala ya yi mata bushara da haihuwarsa, ta kuma gani a zahiri saboda haka babu yadda za’a ta kyamaci wannan abin haihuwa. Allah Ta’ala ya yi mata baiwa da kyawawan halaye na musanman, wanda kuma shi haihuwar Annabi Isah (AS) ba karamar mu’ujiza bace. Da yawa wadansu sun jahilci haihuwar Annabi Isah (AS) ne, shi yasa da dama wasu ke ganinsa a matsayin bakon abu.”
Cikin jawabin nasa ya kara da cewa; “Lokacin da labari ya isa gari cewa ga fa Maryam da da! Al’ummar gari sun yi ta tambayarta cewa, ya aka yi kika samu wannan yaron? Inda nan take tayi masu nuni da cewa su tambayeshi (shi yaron da ta haifa) kenan. Ya bayyana masu cewa, shi bawan Allah Ta’ala ne. Kuma dan sakon da Allah ya aiko masu dashi. Wasu nan take suka yi imani dangane da irin mu’ujizozin da suka tarar dangane dashi. Inda wadansu kuwa suka butulce tare da fandarewa akan abin da ya fadi dags bakinsa”. Malamin ya fadi wadansu mu’ujizozi da suka faru a yayin haihuwar Annabi Isah (AS), ya kuma bayyana cewa, Allah Ta’ala ya yiwa Annabi Isah (AS) cewa zai dauke shi zuwa sama. Zai kuma daukaka darajarsa har zuwa ranar dawowarsa duniya, inda daga bisani malamin ya karkare jawabinsa da fadankarwa dangane da bincike akan tarihi da kuma rayuwar Annabi Isah (AS). An kammala taron ne da yammacin jiya Juma’a, inda daga bisani aka yi addu’a aka sallami kowa.
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN