@Ma'asumah Nigeria News Update
HARIN YAN BINDIGA A GABASCIN SHINKAFI DA ISA: DAGA GANAU BA JIYAU BA.
________________________________
Shinkafi Media Watch
________________________________
Da marecen jiya Talata ne gabascin Shinkafi da Isa suka fuskanci tashin hankali mafi muni a tarihin kafuwar yan bindiga a wannan yanki wadanda ke cin karensu babu babbaka.
Labarin ta'addancin yan bindiga ya bayyana ne da safiyar yau Laraba da garuruwan Shinkafi da Isa suka cika da yan gudun hijira.Ganin wannan cikowar ya tayar da hankalin mutane sosai duba da yanayin da yan gudun hijirar ke ciki na alhini da rashin kwanciyar hankali.Wasunsu na tafiya ne dauke da kaya, kananan yara,tsoffi da dabbobi! Abin tausayi ma wasu basu ma san ina zasu je ba jiqe da ruwan gulbin da suka keto cikin tashin hankali domin tsira da rayukkansu!
Wakilan shafin Shinkafi Media sun yi tattaki zuwa bakin gulbi a gabascin Shinkafi gulbin da ya raba Shinkafi da Kamarawa ta Karamar hukumar mulkin Isa ta Jihar Sakkwato domin ganewa idanu halin da al'ummun wannan yanki ke ciki.
Wakilan Shinkafi Media sun labarta muna irin yanda suka taras da mutane hululu abin ban tausayi wasu a tsaye,wasu a zaune,wasu ma suna bacci musamman kananan yara cikin yanayi na wahaltuwa,kunci da damuwa.
Shinkafi Media ta samu zantawa da wasu daga cikin wadanda abun ya shafa,wadanda su ganau ne ba jiyau ba,kuma sun bayyana irin bala'in da suka gani tun daga yammacin talata har zuwa wayewar safiyar laraba.
Garuruwan da abin ya shafa wadanda zuwa yanzu da muke hada wannan rahoto babu mutum ko daya a ciki sai su yan bindigar sun hada da: Bafarawa,Kamarawa(Tsohon gari da sabon gari),Dangwandi,Garin Fadama,Tsaika,Gebe da Suruddubu duk a karamar hukumar mulkin Isa dake jihar Sakkwato.
Shinkafi Media ta fara tattaunawa da Mazaunin garin Kamarawa wanda ya labarta muna yanda abun ya faru cewa kusan yan bindigar sun raba kawukansu ne zuwa garuruwan da suke son tayarwa ne! " Mu a Kamarawa wasu sun ma shiga sallar Magriba ne wasu kuma basu shiga ba,wasu sun fara sallar amma sallar bata samu kammalawa ba! Duk inda kake karar harbi kawai kake ji abinda ya sanya mazauna gari shiga cikin yanayin tsoro,razani da tashin hankali" Inji shi.
"A lokacin da suka dan tsagaita harbi sai mutane suka fara guduwa wasu na shiga daji,wasu na fadawa ruwa domin su ketaro zuwa Shinkafi,su kuma a lokacin sai suka fara shiga gida-gida suna kora dabbobi! In takaita maka dukkaninmu babu wanda ya kwana a gida,mafi yawancin mutane sun kwana ne a jeji sai da sanyin asubahin aka fara fitowa daya bayan daya zuwa bakin gulbi.Idan sun hadu da kai zasu anshi waya da kudi,ni da nake baka wannan labari har da marina aka yi,kuma wanda ya mareni ya wayeni na wayeshi,bilhasali ma cemun ya yi naci albarkacin sanin da aka yi mun da ya aikani lahira" inji Mazauni garin Kamarawa.
Shinkafi Media ta tambayi ko da asarar rayuka? Yace "Eh! a sabon garin Kamarawa an kashe mutum daya a lokacin da suke harbin kan mai uwa da wabi,a Gebe ma sun kashe mutane biyu,an raunata wasu da harbin bindiga da kuma sara da adda" Inji shi. Haka kuma Shinkafi Media ta tambaye shi ko sun samu dauki daga jami'an tsaro? Sai ya ce "A'a! Zuwa yanzu da nake magana da kai babu jami'in tsaron da ya tsallaka da sunan agaji! Amma yanzu ka gansu nan suna zuwa daukarmu hoto! Tun 5:15 na yamma Mahara suke cin karensu babu babbaka har wayewar safiyar yau laraba babu dauki daga bangaren gwamnati.
Shinkafi Media ta zanta da wani da ya sha da kyar a garin Bafarawa wanda ya labarta muna cewa; " A tarihin rayuwata ban taba ganin tashin hankali irin na yau ba! An shigo gidana na kama Katanga anyi mun ruwan wuta amma Allah ya kareni,na dira makwabta a chan ma na taras ana kwance shanu daga turakunsu,an buda mun wuta amma ba a sameni ba na dira gida na gaba shima hakan ta faru sai da na dira gida na hudu sannan na tsira da rayuwata" Inji mazaunin Bafarawa.
Zuwa 12:00 na rana wakilan Shinkafi Media suna bakin gulbi kuma jirgi na shawagi yana jefa abubuwan fashewa,Mazauna garuruwan sun shaidawa Shinkafi Media cewa inda suke jefa Bama-Bamansu daban inda Maharan suke daban! A cewarsu yanda Maharan ke tsoron jirgin da gwamnati da gaske take a yaki da Mahara sai ta zuba sojoji a kasa ya kasance ana yakin sama da kasa ne a lokaci daya,amma muddin yakin ya kasance a sama ne babu ranar da wadannan mahara zasu barsu su zauna lafiya.
Wani mazauni Dangwandi da ya samu fitowa ya labarta muna cewa,zuwa 4:30 na yamma wasu mazauna garin Tsaika da Dangwandi sun lallaba domin debo kayansu amma mahara sun hana su fitowa,abinda suke cewa wai ba zasu tafi su barsu su kadai ba! Kuma Maharan sun labarta masu cewa abinda yasa sukayi masu haka wai cewa sun munafuccesu,domin sune suka sanya ana turo jirgi yana tayar masu da hankali a saboda haka suma shi ne dalilin da yasa suka tayar masu da hankali.
An dai samu asarar rayukka,an samu raunukka,an kuma kora dabbobi da zuwa yanzu ba a san adadinsu ba!
Allah ya tausaya muna ya kawo muna karshen wadannan musibu da suka ki ci suka ki cinyewa.
Allah muna rokonka duk masu hannu a wannan hare-hare Allah ya tona masu asiri,Ya wulakantasu,Ya kaskantasu duniya da lahira.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Labaran Duniya