@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN KANA DA ALMAJIRAI KA SAMU KAYAN NEMAN KUDI
Almajiranci a zamanin baya abune mai kyau da ban sha'awa, kuma su suka fi cancanta da a taimake su.
Ko yayi ma dadi ko kaji haushi ko kuma kayi zagi duk daya ne, amma harkar almajiranci a wannan zamani babu abin sha'awa sai dai zubar da mutuncin muslumci da musulmai.
Bangare uku duk suna da matsala ta wannan fanni.
(1)- IYAYEN YARA:- Gaskiyar magana suna tura yaransu makaranta ne kawai don neman samun sauqin daukar dawainiyar su ba wai don su sami karatu ba.
Hujjata anan ita ce, sun tara 'ya'ya da yawa a gabansu sun kasa sauke haqqinsu da ya hau kansu, saboda haka sai su tura su makaranta don neman sauqi. Ta yadda za ku gaskatani shine, za kuga iyayen yaran basa tallafawa malaman da komai bayan kai yaran nasu, sannan ba sa sayen wani abu su aikawa yaran na omo ko sabulu.
MALAMAI:- Musamman a wamnan lokaci na damina, sai kaga malami da almajirai sama da 30 a gona suna noma zuwa 12;30pm, amma idan sun dawo gida ko kunu ba za a basu su sha ba. Suna yasar da fartanya za su dau robar bara zuwa gidajen mutane da gudu 🏃♂️🏃♂️🏃♂️!
Tsammanin ku jama'ar ce za ta ciyar muku 'ya'yanku ko almajiranku alhali ku suke yiwa noma kuna tara kudi?
ALMAJIRAI :- Duk da cewa ciyar da su ba haqqin jama'a bane na iyayensu, su dai kawai haqqin da ya hau kansu (jama'a )suyi taimako ne in suna da hali.
Amma wani abin haushi shine, idan almajiri 👨🏽⚖️ yayi bara aka ce masa yayi haquri sai ya kalli idonka ya fashe da kuka 😂😂😂 memakon yayi haquri.
Abinda na kasa ganewa shine, shin so suke a basu babu ko me suke nufi?
Ko kuma dai rashin adalci ne irin nasu? Domin in abin zargi ne ko yin kuka, sai suje wajen malaman da suke yiwa noma suna barinsu da yunwa suyi musu kukan. Ko kuma su koma gidan iyayensu suyi musu kukan, don haqqinsu a wuyansu yake.
DUK IYAYE DA MALAMAN CUTAR DA YARAN SUKE YI BA SAUKE HAQQI BA .
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
LARABA, 8th July , 2020/ 17-11-1441
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN