@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ALLAH NA KARBAR ADDU'AR 'DAYANKU MATUQAR BAI YI GAGGAWA BA
Raunin zuciya kan sa mutum ya yanke tsammani daga rahmar Allah , alhali a ko da yaushe shi mumini ba ya yanke tsammani daga rahmar Allah .
Alqawari ne na Allah (T )cewa mu roqe shi zai amsa mana, kuma Shi ba ya saba alqawarin Sa, sai dai dan adam ya kasance mai gaggawa ne.
Babu tilasci cikin ganin damar Allah wajen aiwatar da wani al'amari nasa ko rashin aiwatar da shi, amma dabi'ah ce ta mutum a kullum yaga ya sami abinda yake so a lokacin da yake so, shi kuma al'amarin Allah ba haka yake ba. Da ya kasance mai biyawa mutum buqata a duk lokacin da yake buqatar wani abu, to, da ya tashi daga matsayin Allah zuwa matsayin wanda ake da iko a kansa.
Annabi Ayuba (A.S )ya taba roqon Allah wata buqatarsa kuma ya amsa masa, amma bai ga ijabar ba har sai bayan shekara 40. Dalili kuwa shine, Shi Allah (T )ya sanya komai nasa bisa ajali ne, kuma ba ya zartar da shi har sai ajalin nasa ya cika.
Wannan dalili yasa Manzon Allah (S.A.W.W )ke cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ ANA AMSAWA 'DAYANKU MATUQAR BAI YI GAGGAWA BA, YANA CEWA;HAQIQA NA KIRAYI UBANGIJINA AMMA BAI AMSA MIN BA .‘’
Saboda haka kada gaggawarka tasa ka zargi Allah kan abinda ya fada cewa mu kiraye shi zai amsa mana, wanda bai ambata maka lokacin amsawar tasa ba.
Shi alqawarin Allah gaskiya ne, kuma ba ya saba alqawarinsa. Abinda ya hau kanmu kawai shine mu nemi amsawar tasa kuma muyi imani da Shi .
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Monday, 20th July, 2020/ 29-11-1441.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Tunatarwa