Abu Turab, Sunan Da Imam Ali (A.S) Yafi So Kenen A Rayuwar Sa!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

WAI GASKIYA NE IMAM ALI (A.S )NA FUSATA SAYYIDAH FATIMA (S.A )?

Yazo cikin dukkan littafan musulmi shi'ah da sunnah cewa Annabi (S.A.W.W )ya sha bayyana cewa Sayyidah Fatimah (S.A)tsoka ce daga gare shi, kuma duk wani abinda ya cutar da ita yana cutar da shi, kuma yana fushi da wanda ya fusata.

Kuma ya tabbata cikin littafan tarihi cewa Sayyidah Fatimah (S.A )har ta bar duniya tana fushi da Abubakar sakamakon hana mata gadon mahaifinta (S.A.W.W )da kuma yin tawayensu ha wasiyyar mahaifin nata.

Sannan yazo cikin Sahihul Bukhari cewa wai wani sabani ya taba shiga tsakanin Imam Ali (A.S )da Sayyidah Fatimah (S.A )wanda hakan ya fusatata.

Ga dai ruwayar kamar haka;

Daga Sahal Bn Sa'ad yace, ‘’ BABU SUNAN DA ALIYU YAFI SO FIYE DA ABU TURAB, KUMA YA KASANCE YANA FARIN CIKI IN AN KIRA SHI DA SHI .‘’ Yace,

Wata rana Manzon Allah (S.A.W.W )yazo gidan Fatimah (A.S )amma bai sami A liyu ba a cikin gidan, sai yace;

‘’ INA 'DAN AMMINKI ?‘’ Tace,

‘’ Wani abu ya faru a tsakaninmu sai ya fusatani, shine ya fita bai tsaya a wajena ba.‘’

Sai Manzon Allah (S.A.W.W )ya cewa wani, ‘’ JE KA DUBO A INA YAKE ?‘’ Sai yazo yace,

Yaa Ma'aikin Allah, yana cikin masallaci a kwance. Sai anzon Allah (S.A.W.W )yazo ya tarar da shi a kishingide mayafinsa ya fadi daga gefensa, turbaya ta zuba a kansa. Sai Manzon Allah (S.A.W.W )ya riqa share masa qurar daga jikinsa yana cewa,

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ TASHI ABU TURAB, TASHI ABU TURAB .‘’

(Bukhari, hadisi me lamba 6280)

          TAMBAYA

- Shin da gaskene ya fusata Fatimah amma Annabi (S .A.W.W )yake rarrashinsa?

- Anya kuwa ba so ake a nuna cewa shima yana daga cikin masu fusatata bane don a toshe bakin masu ambaton wadanda suka cutar da ita ba?

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

Saturday, 25th July , 2020/ 5-12-1441

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post