Hannun Ka Mai Sanda: Yan Uwa Mu Lura, Akwai Darasi Mai Tarin Yawa A Cikin Wannan Maganar



A shekarun baya lokacin Sheikh Zakzaky (H) yana cikinmu, Wani Dan uwa matashi ya taba zuwa gidan Sheikh Zakzaky (H) ya tare da zama a chan. Sai wata rana Malam (H) ya kira Dan uwan nan yayi masa wasu yan tambayoyi kamar haka: A wani gari kake Dan uwan ya bashi amsa, Meye kazo yi a nan bayan kai ba Haris bane bare muce kazo duty ne? Sai Dan uwan yace "nazo ne domin neman Sabati da yardar Allah".

 A wannan yanayin sai Malam (H) ya qara tambayarsa meye sana'ar Mahaifinka? Sai Dan uwan yace "Mahaifina Manomi ne" a nan take Malam (H) yace to ka tattara ka koma gida ka cigaba da yiwa Mahaifinka hidima domin a nan ne Sabatin yake da kuma nuna kyawawan dabi'u. Wannan Dan uwan ya koma gida yayi amfani da maganar Malam (H) har ya zama a duk cikin yaran Mahaifinsa babu mai bada gudummawa a bangaren sana'ar baban nasa (Noma) kaman shi, ba dadewa da yin hakan Allah ya azurta shi da samun Shahada.

 'Yan uwa mu lura akwai darasi mai tarin yawa a cikin wannan maganar.

 - Ibrahim Almustapha Saminaka
 - 14/July/2020

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post