Zauren Kairul Amal Ya Sami Shaida Ta Musamman Daga Mu'assasatus-Shuhada



A bana ma, 'Yan uwa na Zauren KHAIRUL AMAL da ke WhatsApp sun amshi takardar shaida daga Mu'assasatus Shuhada dangane da Infakin Shuhada da suka shiga a matakin ajin Khalilullah.

Shugaban Mu'assasar, Shaikh Abdulhamid Bello ne ya mikawa 'Admin' din zauren na Khairul Amal, Saifullahi M. Kabir a yau Talata a yayin taron karawa juna sani na wakilan Mu'assasatus Shuhada din yankin Jos da ya gudana a garin Saminaka.

A yayin jawabinsa, Shaikh Abdulhamid Bello ya yi kira ga yan uwa akan su fahimci ma'anar hakkin Shuhada'u kuma su lizimci sauke shi don Allah.

Shaikh din yace: "Lokacin da aka assasa Mu'assasatus Shuhada, muna da Shahidi 1 ne da 'ya'yan Shahidai 6, yanzu kuwa akwai Shahidai 1027 wadanda ake da tabbacinsu. Akwai kuma ya'yan Shahidai 2370. Akwai matan Shahidai fiye da 550. Akwai iyayen Shahidai fiye da 1700, wadanda dukkansu kowanne akwai aikin da Mu'assasatus Shuhada ke musu."

Ya kara da cewa: "Kafin Wakiar Zariya 'ya'yan Shahidai ba su kai 500, yanzu kuwa sun doshi 2500. Kuma kashi 80% dinsu dalibai ne da suke karatu a makarantu daga Firamare har zuwa Jami'a."

Yace, ka ga dawainiya da hidindimunsu yana ninkuwa ne sosai a kowane lokaci, musamman batun karatu, tarbiya da kuma bukatun rayuwa.

Wannan ne karo na uku da Zauren Khairul Amal ke shiga wannan ajin na matakin Khalilullah a jerin Infakin shekara-shekara na Mu'assasatus Shuhadau.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post