Kwanaki nake ganin Rubutu wani Mutum, ba Dan uwa bane, a cikin rubutun nasa yake cewa "Su 'Yan Shi'a sai lokacin Ghadeer yazo su cika mana kunne da cewa ay babu yanda za ayi Manzon Allah ya tafi ba tare da ya bar wani Wakilinsa ba, wanda zaiyi magana da yawunsa. Amma yanzu sai gashi su Jagoransu baya nan amma babu wanda ya bari yake magana a Madadinsa, sai wannan rubutun nasa ya sosa min zuciya.
To na farko dai su wadannan Jahiliyyan sunyi amfani da yakin ruwan sanyi wajen bata tunanin 'yan uwa. Su suka bata Sheikh Yakubu Yahaya a wajen 'yan uwa ta hanyar nuna musu cewa shi bai damu da al'amarin Jagora ba! Ya kaucewa Da'awar Malam. Wanda Sheikh Yakubu shine tun farkon wannan Waki'a din yayi ta shiga yana fita a Gidajen Radio, Jagorantar Muzaharori, ta janibin Shari'a da dai sauran su. Malam Yakubu da su ake wannan Harka tun farko har zuwa yau, sun samu ingantacciyar tarbiyya kaitsaye daga su Malam (H) amma a halin yanzu anyi amfani da yakin ruwan sanyi wajen bata sunansu a cikin yan uwa musamman matasa.
Sannan sunyi kokari wajen bata sunan Ibrahim Musa wanda ya kasance tun Sayyid (H) yana nan shine yake magana da sunan Harka a kafafen Sada Mumunta. Sun bata suna shi ta wanda yanzu da yawan yan uwa musamman Matasa basa ganin sa a bakin komai a Harka din. Yanzu ya zama su wadannan Malaman namu da suke tare da su Malam (H) tun farkon Da'awa har yanzu basa iya fitowa suyi magana da yawun Harka Islamiyya saboda wannan tunanin da a cusawa 'yan uwa.
- Kadan daga cikin Jawabin da aka gabatar yau 29/June/2020 kenan a wajen taron kyautata Alaka tsakanin Harisawa da sauran bangarorin Harka Islamiyya a Da'irar Saminaka.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN