Ya Gina Gidan Da Mutum Huɗu (4) Suka Kasa Ginawa A Garin Guda!!!






@ MA'ASUMA NIGERIAN NEWS UPDATED @

SIYASA ZANCEN BANZA

Duk da irin matsalolin da ke qunshe cikin siyasa da 'yan siyasa ba zai hana ka yaba abinda wani dan siyasa yayi ba.

Garin Guda wani qauye ne a qaramar hukumar Ningi ta Jihar Bauchi, tsakaninta da cikin garin Ningi kilomita hudu (4km )ne.

Bisa ganin damar Allah ba wai bisa isarsu ba suka sami daukaka na samun zababbun 'yan siyasa da suka riqe kujerar majalisa ta mazabar Ningi ta tsakiya a gwamnatin jihar Bauchi.

A lokaci guda an sami dan majalisa da sanata daga cikin garin Guda a lokacin gwamnatin Obasanjo gwamnatin da tayi wadaqa da kudade yadda kowa ya san da wannan.

Bayan tafiyarsu an qara samun wani dan majalisa da suka hau kujera daya da arrister M.A kuma suka tafi tare.

A halin da muke ciki yanzu garin Guda ta qara samun dan majalisa daga cikinta wanda ke riqe da kujerar kakakin majalisa (speaker )a jihar Bauchi.

Iya baiwa da nuna qauna an samu daga Ubangiji mai yin yadda yaso, sai dai abin takaici cikin wadannan mutane 4 ba suyi ko ajiye wani abu wanda qimarsa takai #1000 cikin garin Guda da za a nuna cewa wannan romon siyasa ce ta wane ba.

Abdurrazaq Nuhu Zaki dan majalisa ne a qaramar hukumar Warji da ke qarqashin masarautar Ningi ta jihar Bauchi, kuma ya wakilci Ningi da Warji a matsayi (house of representative ), yanzu kuma shine (commissioner , ministry for local government and chieftaincy ). Amma wannan bawan Allah ya sayi babban fili (MAQABARTA )a garin Guda tun zamanin baya ya mallakar musu a matsayin gidan da ake bisne 'ya'ya, 'yan'uwa da sauran dangin wadannan mutane 4 da ma sauran al'ummar gari.

Yanzu duk lokacin da aka shigar da wani cikin wannan gida sai an tuna da wannan bawan Allah tare da yi masa addu'a.

Ba siyasa nake ba ballantana na yiwa wani campaign, amma haqqi ne akan dukkan mai adalci ya fadi gaskiya ko akan waye.

KO AKWAI MAI IYA FITOWA YA MUSANTA WANNAN MAGANA?

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post