SHIN KO KUNTUNA DA MAGANAR SHEHI SHEKARU BIYU DA SIKA SHIGE
Babban malamin nan a Najeriya Sheikh dahiru usman Bauchi yayi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da a zauna domin tattaunawa game da Shugaban kungiyar shi’a El-zakzaky. A cewarsa ya kamata a samu mafita domin a sake shi ya je ya nemi lafiya, idan har gwamnati tayi haka to lallai babu shakka za'a kara samun zaman lafiya a kasar.
Shehin malamin yaci gaba da cewa kin sakin El-zakzaky wata jarabawa ce da Allah zai jarabci wannan kasar da ita, saboda shugaban shi’an malamine na addinin musulunci, sannan kuma tsare shi ba tare da wata hujja ba ,kuma ba'a nuna alamar yana da laifi ba ,to lallai Allah zaiyi fushi da wannan kasar.
Sheik Dahiru Bauchi ya kammala bayanansa da cewar malamai dai sune magada annabawa idan aka muzguna masu to babu shakka za'a fuskanci fushin Allah, kuma shi fushin Allah babu dan ba ruwa na kowa da kowa zata shafa.
Daga karshe shehin ya bawa gwamnati shawara data saki El-zakzaky a nema masa lafiya a kasar waje.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN