=============================
A tarihin Nijeriya ba a ta6a samun Shugaban kasar da ya zubar da Martabar Kasar nan da Kimarta a idon Duniya lokacin mulkinshi Kamar Shuga Buhari ba.
Duka shuwagannin da mukayi a wannan Kasa tamu, suna kwatantawa wajen kokoarin yin biyayya ga Kundin tsarin mukin kasar, amma shi shugaba Buhari fito na fito ma yake yi da tsarin mulkin, kuma dolayen 'yan majalisarmu sun zura ido suna kallonsa.
A lokacin mulkin Buhari ne kawai 'yan Najeriya suka fara sanin suyi hijira su tsallaka makwabtan kasashe wajen neman agaji da mafaka, akan matsalar rashin tsaro da kisan kiyashin da ake yi musu, musamman a yankin Arewa maso Yamma. Shekaru biyar 'yan Nijeriya suna cikin wannan yanayi, har yau babu abunda gwamnati take ta6ukawa akan wannan lamari. Wannan Abun kunya ne babba.
A zamanin mulkin Buhari ne Dan Nijeriya ya fara ganin gwamnati tasa Sojojin Kasar suna harbin 'yan kasar da harsahi mai rai, su kashe har La'ila (kuma wa'enda ake kashewar 'yan kasa ne (Innocent) wae'enda basu dauke da wani makami). Wannan Babban abun Kunya ne ga duk 'Dan Nijeriya!
A zamanin mulkin Buhari ne aka fara samun 'yan Nijeriya sun kai gwamnatin kasar kara sabo da muzguna musu da Jami'an tsaron kasar keyi, Karo na farko, a gaban kotun Duniya. Wannan Babban Abun kunya ne.
A zamanin mulkin Buhari ne kawai 'yan Nijeriya suka fara ganin an tura bataliyoyin Jami'an tsaro ('Yan sanda) da yawansu ya Kai dubu Talatin (30,000) don ayi amfani dasu wajen kwace kujerar Gwamna a wata jiha, amma aka gagara tura koda rabin wannan bataliya a wuraren da 'yan ta'adda suka fake suna gallazawa al'ummar kasar. Wannan Abun Kunya ne babba.
A Nijeriya ne, kuma a lokacin Mulkin Buhari, aka fara samun wani 'Dan kasa ya kai gwamnatin kasar kara a gaban kotun kasar, akan wani zaluncin da aka yi masa, kuma kotu ta yanke hukunci, cewa; lallai an zalunceshi, kuma gwamnati ta biyashi diyya akan zaluncin da tayimasa, amma gwamnati ta tsallake wannan hukunci na kotun kasa, wadda ke hukunci da kundin tsarin mulkin kasar. kuma taci gaba da zaluntar wanda ya kai karar. Wannan ba Karamin abun Kunya bane.
A zamanin mulkin Buhari ne kawai muka ta6a ganin yunwa tana kashe 'yan kasa saboda hanasu fita neman abinci da gwamnati tayi akan cutar Korona, kuma ta gagara tallafa musu da ko kwabo, a daidai lokacin da muka ga sauran kasashen Duniya suna baiwa 'yan kasar makudan kudi don rage radadin zaman gida. Wannan babban abun Kunya ne.
Gaskiya wannan tsoho ya tozarta wannan kasa, da nutanen Kasa a idon Duniya.
Sharief Munauwar Mukhtar Gusau
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN