Tauhidi Buhariyya: Wai Wane Allah Kuke Nufi, Ko Dai Wani Sabon Karatu Ne?



======================

Matsalar tsaro kullun sai kara ta6ar6arewa takeyi a Arewacin Nijeriyya inda mafi yawan Musulmin kasar suke rayuwa, rayuwar al'umma ta zama kamar kitse a bakin wuta, kullun sai 'yan ta'adda sun kashe mutane, sun lalata dukiya amma gwamnati ta kasa ta6uka komai akan lamarin, Kuma saboda renin hankali idan kayi magana, sai a ce maka wai daga Allah ne!

A shekarun baya; babu irin zagin da 'yan Arewa basu yiwa gwamnatin da ta gabata akan matsalar harakokin tsaro ba. Da zarar Bom ya tashi, sai mu hau zagin Jonathan da gwamnatinsa, wasu ma sai kaji suna cewa; “Wannan shegen arnen, don shi ba dan Arewa bane, shiyasa ya zura ido ana kashe 'yan Arewa”. Kai a kasarnan akwai ma manyan Malaman da har Alqunuti suka rika yi a masallatan Khamsus-Salawat, suna tsinewa Jonathan da PDP akan matsalolin tsaro, duk dai wanda zaka ji yayi magana, to, zakaji baya kawo Allah a wancan lokacin, sai dai ya jingina laifin ga gwamnatin Jonathan.

Lokacin mulkin Jonathan an kashe mutane mun ce laifin Jonathan ne. Yanzu (Lokacin Mulkin Buhari) ana kashe mutane fiye da lokacin Jonathan, amma kun ce daga Allah ne! Shin abun tambaya anan shine; Shin a lokacin Jonathan babu Allah ne!? Ko yayi tafiya ne a wancan lokacin shiyasa muke jingina abun ga Jonathan, yanzu kuma da Buhari ya hau mulki sai Allah ya dawo daga tafiyar da yayi, shiya yanzu sai ake jingina abun ga Allah???

✍️ Sharief Munauwar Mukhtar

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post