:
Sa'kon Ahlulbaitias ﺭﺳﺎﻟﺔ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﺒﻴﺖ ﻉ the Message of Ahlulbayt a.s.
-------------_------------
*Shaheed Zakariyya Lawal Dabai*
================
Mun iso gyallesu Magriba ta kusa muka wuce gidan baki kai tsaye muka iske mutanenmu (Harisawan Kudan Unit) sun cika gidan ana zaune ana ta bada bayanin abinda ya faru a Husainiyya can zuwa Magriba sai ga su Malam Rabi'u Ahmad da yayansa Umar Ahmad Dabai, Hamisu Muhammad, Ishaq Aliyu, Kabir Umar, Sagir Kabir da sauran yan uwa sun iso. Muna zaune har wajen takwas na dare bamu samu munyi sallah ba ballantana cin abinci mutane kuma keta karuwa babu kakkautawa can sai ga sanarwar cewa duk wanda ya zo bada kariya yayi maza yaje Kofar gidan Malam (Central na Harisawa) ya bada Sunansa don a bashi duty ko aikin da ya kamata, duka gidan muka nufi kofar gidan Sayyed Zakzaky muna isa aka dasa dogon layi kowa na shiga yana bada sunansa gari da kuma Unit Ko Zone dinsu. Duk wanda aka dauki sunansa sai ya fito an cika kofar gidan Sayyed makil ko'ina yan uwa ne.
Can sai muka fara jin karar harbi akace ga sojoji nan sun iso gate din Banadeen (Gate din wajen Congo Campus) har sun harbi harisawan dake duty a gurin (Mangwaron Andy).
Nan fa yan uwa muka nufi gate din, nan da nan kuma aka dauke wutar lantarki anguwar tayi baki kirin sojoji kuma kamar an basu damar kara kaimi na kisa tunda ga duhu yayi sai suka rinka harba wani abu kamar knockout mai wuta da tsananin haske yana kamawa sai su budewa yan uwa wuta tas tas tas babu kakkautawa.
Cikin daren nan sunyi barna marar adadi sun shahadantar da yan uwa marar adadi cikin daren Shaheed Hamza Yawuri yayi shahada tare da ba'adin yan uwan masu yawa.
Barin wuta ta kudu, bariki barin wuta suke da karar manyan bindigu, gabas ma wajen FCE barin wuta, yamma ma wajen Mangwarori harbi, sun kewaye gidan Sayyed ta kowanne bangare. Ba a yan mintuna ba a dauki shahidai ba.
Sojoji karo karfi kawai suke cikin daren nan don haka kisa suke babu kakkautawa in mun dannasu sunyi baya kamar sun gudu sai kuma su fake bayan tankokinsu suyi ta harbin yan uwa.
Haka akayi ta dauki ba dadi dasu cikin daren nan an sami shahidai sama da dari biyu banda wadanda suka sami munanan raunuka
babu adadi, kana iya jiyo karar harbe-harben da sojoji suke a Husainiyya cikin daren nan da kuma lokacin da suka harbeta bom.
A ranar anyi tsananin sanyi mai shiga jiki, haka yan uwa ke zazzaune a layi da kewayen gidan Abba (h) wasu kuma yan uwan na salloli, suna kiran iyalai da yan uwa suna ban kwana da fada masu halin da ake ciki, yan uwa mata suma suna tattaro duwatsu da baraguzan gini suna mikawa burazu na kariyar kai.
Haka muka kwana babu dadi hardai zuwa kiran sallar asuba sannan harbin nan ya dan tsakaita da kyar muka yi sallah wasu ma sallar bata yiwu ba, sojojin fa suka cigaba da harbi da kuma dannowa ana dannasu zuwa gidan Malam, tunaninmu idan gari ya waye mutanen nan zasuji kunya su gudu a sami damar dauke shahidai da wadanda sukaji mummunan rauni, amma ina ashe da can ba ayi komai ba yanzu ne sojoji zasuyi kisan.
Wallahi ban taba ganin tashin hankali ba irin na wannan ranar ko a cikin film din American ban taba jin tsananin barin wuta irin wannan ba
da yake ni ina dai-dai gate din transformer jin "Teckon international school" gate da yan Abul Fadhl Abbas suka kafa nan ne akayi bari wuta na rashin hankali da imani ba a mintuna ba a sami shahidai, da guri yayi guri duk sakwan biyu zuwa uku shahidai na faduwa.
Sojoji suna amfani da wani irin mugun harsashi na musamman da ya kai tsawon yatsan mutum idan suka harboshi ya sami dan uwa sai yayi sama sannan dan uwa zai fado kasa.
Sunfi harbin gurare uku a jikin yan uwa kodai su harbi kai ko kirji ko ciki wanda nan take mutum zai yi shahada.
Duk da wannan tsananin ruwan wutan yan uwa sunyi tirjiya iya tirjiya, sojoji sun fuskanci tirjiya a gate din nan duk kusan gawarwakin shahidanmu da sukayi kaca-kaca harbin nan gurin ne.
Ana tsakar ruwan wuta nan Shaikh Turi ya ciro alkyabbarsa da babbar rigarsa ya fito ya tunkari gurin sojojin nan, yan
uwa ana rikeshi Shaikh yana fadin babu wani abu zai je ne gurin sojojin nan ne yayi magana dasu yanzu zai dawo yan uwa na kuka ganin wannan babban tashin hankali, Shaikh na cewa yau ba ranar kuka bane yau ranar cika alkawari ne daga baya aka aiko cewa Sayyed na kiransa yaje ya dawo yace indai ba sojojin nan sun tafi bane kada wani ya kara zuwa yace masa ana kiransa, Shaikh Qasimu Umar Sokoto yana kabbara yan uwa muna amsawa muna dannawa tun muna da yawa har muka koma yan kwarori sojoji kuma kisa kawai suke babu kakkautawa.
Muna cikin wannan halin aka harbi Malam Rabi'u Ahmad a hannun hagu yayansa kuma Umar Ahmad a cinyarsa ta hagu, don haka dani da wasu yan uwa muka kamosu muka nufo gidan harisawa.
Mun tafi kai su gidan harisawa babu guri shahidai ne kawai cike da gidan haka nan gidan Malam Maina shahidai ne kwance, haka muka rabasu suka kwanta a kasa.
Muna tare dasu Malam Rabi'u Ahmad da Umar a gaban Dr. Mustapha yana masu aiki sai muka hangi gidan Sayyed na ci da wuta daga kudu nan fa Dr. Mustapha yace yan uwa babu yadda zamu iya kowa ya fita yayi iya abinda zai iya shi kam yana nan ba zai je ko'ina ba sai dai su zo su iskemu har nan su shahadantar dani, nayi kokarin na tallabi Malam Rabi'u mu fita daga gidan tunda mun hangi sun sanya wuta yace min gaskiya ba zai iya tafiya ya bar dan uwansa Umar Ahmad ba kawai mu tafi sojojin in su zo su karisasu.
Haka muna ji muna gani muka barsu muka fito layin gidan Malam sai dai-daikun yan uwa kawai sai kuma tarin shahidai ko'ina a kofar gidan Sayyed.
Muna fitowa muka shiga gidan nan na yamma da gidan Sayyed na jikin masallaci, matar gidan da mijinta suna cikin daki kulle amma suna jin motsin shigowarmu suka fara zaginmu, zagin rashin imani da tausayi, mai gidan na ihu na mana barazanar kodai mu fita muje su kashemu ko kuma shi zai kira mana su su kashemu a gidansa.
Dole muka fice muka dawo layin gidan Sayyed babu kowa lokacin sojoji sun fara kewaye gidan ruwan wuta suke na rashin hankali da imani babu sassauci maza mata yara kowa yaje kasa.
Muka bi ta wani lungu mutanen anguwa suna kawo mana farmaki dole kabar anguwar ko kuma su mutanen anguwar su karisaka da kansu,
da kyar wani matashi ya shiga damu gidansu bayan jayayya dashi ya taimakemu ya bamu ruwa muka wanke jinin jikinmu ya dauko wasu kananan kayansa ya bamu yace mana shima yana zuwa Husainiyya kuma har budurwa yana da ita yar shia don haka ya taimakemu ya shiga gaba muna biye dashi har muka fito bakin Tudun Wada kana hangen gidan Sayyed yana ci da wuta wallahi babu abinda zamu iya.
Wani abu da zan iya tunawa a gate din transformer da na turo hotunansu anyi wani abu da duk sadda na tuno shi ya kan tayar min da hankali, lokacin da wuta tayi wuta kowa yana ganin zai yi shahada wani dan uwa yace don Allah akwai mai mota cikin yan uwa, nan take wani yace masa E yace to ya sadaukar masa da ita don Allah nan take ya bashi makullinta yace a sami yan uwa da zasu taimaka masa zai tunkari wannan azzaluman suyi kunar bakin wake gurin taka masu birki da jikinsu, ya hau motar yayi key yan uwan uku suka shiga yayi kan sojojin nan da suka fuskanci niyyarsa na dakatar dasu sai kawai suka harbe motar da RPG nan take ta tarwatse da dukkan yan uwan da ke ciki.
Hatta loudspeaker da sojoji suka rinka izgilanci da ita bayan sun kashe kowa sun zo kofar gidansu Sayyed ta yan uwa ce, wadda da aka fito da ita domin a rika shajja'a yan uwa da karfafasu a gate din lokacin da kowa ya kwanta kasa imma dai mutum yayi shahada ko ya sume ko yana da raunukan da ba zai iya tashi ba yana kwance, ita suka dauka suna fadin Zakzaky ka fito kafin mu kirga goma 1,2,3,4..... Can kuma sai suce ka fito ko kaji tsoro ne dama karya kake yi da sauran cin mutuncin kala-kala.
Allah ka kara tsinewa Buhari albarka da duk wanda ke da hannu gurin zubar da jinin yan uwanmu
gaskiya wakiar gyallesu sai dai ka fadi dan abinda zaka iya tunawa domin ta wuce duk tunanin mai tunani duk wani nau'i na cin zarafi da take hakkin dan adam babu wanda ba ayi ba a gyallesu wallahi nasha ganin wakia ko ta ratsa dani amma ban taba ganin irin ta gyallesu ba,
Ban taba ganin an dagargaza kan dan
adam ba sai a gyallesu lokacin da Escort din wakilin yan uwa na Gombe Malam Muhammad Abbare ya iso da safiyar lahadin nan yan mintuna da isowarsa wani tsinanne soja ya harbi kansa nan take kwalwarsa ta tarwatse jini yana zuba ta bakinsa da hancinsa yana wani irin kakari jinin na kara fesowa, shi kansa Dr. Mustapha cewa yayi a fuskantar dashi alkibla don babu abinyi, ga wayarsa na ta faman karar kiran yan uwa.
Tun daga bakin gate din Banadeen gawarwakin yan uwa ne ko ina amma babu wanda aka kauda gefen hanya haka sojoji ke bi ta kai suna kara matsowa gidan Sayyed da tankoki da muggan makamansu
saboda tsananin mugunta, harsashin da suke harbin yan uwa na musamman ne in ya sami kankaren ginin gidan Malam Hamza Yawuri ko falwayar jikin transformer sai yayi masa rami.
Ta bangaren mutanen gyallesu kam babu wani sauki ballantana imani ya fi maka sauki ka fuskanci jami'an tsaro da ka nemi taimakonsu don tsananin kiyayyarsu da gabarsu ga Sayyed da almajiransa ba don Sayyed da almajiransa sun taba yi masu wani abu na cutarwa ba.
Duk cutarwa da akayi wa Sayyed Zakzaky da almajiransa da sa hannun mutanen gyallesu da kuma taimakonsu sai dai Allah ya isa tsakanin mu dasu.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
#FREE_ZAKZAKY