Samun Mace Saliha, Yafi Dukkan Abinda Mutum Zai Tara!!!





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

TABEWA TA TABBATA AKAN ZINARI DA AZURFA

Burin mafi yawan jama'ah shine suga sun tara dukiya a duniya don holewa da nuna qasaita , har ma kaji ana cewa ai duk wanda ya mallaki gida, mota da mata ya gama samun duniya .

Ta wata fuskar hakane , amma duk wani abinda mutum zai samu wanda ba zai amfanar da lahirarsa ba, to, wannan abu ba abin farin ciki da alfahari bane gare shi.

Abdullahi Bn Huzail yace, wani abokina ya bani labari daga Manzon Allah (S.A.W.W )cewa yace;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

" TABEWA TA TABBATA GA ZINARI DA AZURFA ."

Yace, yadda abin ya faru shine, abokina yace, sun tafi shi da Umar Bn Khaddab Zuwa ga Annabi (S.A.W.W )sai yace, yaa Ma'aikin Allah , fadinka cewa; " TABEWA TA TABBATA AKAN ZINARI DA AZURFA ."

To, me ya kamata mu ajiye (storing )?Sai Manzon Allah (S.A.W.W )yace;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

" ZUCIYA MAI GODIYA, DA HARSHE MAI AMBATO (Zikiri )DA KUMA MACE WACCE ZA TA TAIMAKI 'DAYANKU WAJEN AIKIN LAHIRARSA."

(Musnad Ahmad, J:5, SH:282 )

Wadannan abubuwa uku da ke cikin hadisin sun fi komai, domin duk wanda Allah ya ba shi zuciya mai godiya ba zai taba zargin Allah cikin dukkan quncin rayuwa da ya shiga ba, kuma zai gode qanqanin da ya samu.

Harshe mai ambaton Allah (da iklasi )ba zai taba barin mai shi ya mance da Allah ba ballantana ya saba masa.

Sannan ita irin wannan mata saliha ita ce wacce a ko da yaushe take qarfafar mijinta wajen aikata abinda zai kyautata masa lahirarsa, kuma ta tsoratar da shi aikata abinda zai kai shi wuta, ba ta buqatar a ciyar da ita da dukiyar haram komai qanqantarta.

Wanda ya sami irinsu ba ya hada su da kowa. Dubi zamantakewar Manzon Allah (S.A.W.W )da Sayyidah Khadijah (S.A ), ko kuma zaman Imam A li (A.S )da Sayyyidah Fatimah (S.A ), sun kasance mata mafi alkhairin abin ajiyewa.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

Juma'ah, 12th June, 2020/ 22-10-1441.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post