Saɓani Kan Ranar Da Aka Saukar Da Ayar Cikar Addini!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ANYI HAKAN NE DON A BOYE WASIYYAR ANNABI (S.A.W.W )TA ZAHIRI

Babu mai kokonton cewa ayar da Allah (T )ke cewa;

‘’ A WANNAN RANA CE NA CIKA MUKU ADDININKU ....‘’ (MA'IDA, AYA TA 5)

Ita ce ayar qarshe wacce aka saukarwa Annabi (S.A.W.W )da ke nuna cewa an rufe hanyar kawo saqo zuwa ga Annabi (S.A.W.W )ta hanyar Mala'ika Jibril (A.S )wanda hakan ke nuna cewa rayuwarsa (S.A.W.W )ta zo qarshe .

Sai dai kuma abinda ya faru a wannan rana ya sosa zukatan wasu har suka qulla niyyar lullube wannan al'amari domin bai zo musu daidai da son ransu ba.

Riwayar farko an samo ta ne daga Fudhail daga Haruna Bn Intirata , daga babansa yace, yayin da aka saukar da ayar ,
‘’ A yau na kammala muku addininku ....‘’ Wannan ita ce ranar Hajji mafi girma ‘’

Wannan hadisi na tabbatar mana ne cewa daga wannan rana babu wata aya da aka saukarwa Annabi (S ), kuma ranar Hajji ne 9 ga Zul-Hijja .

A riwayar Abu Sa'idul Khudri (R.A )kuma yace, ta sauka ne akan Manzon Allah (S.A.W.W )a ranar Ghadir Khum yayin da ya cewa Aliyu,

‘’ DUK WANDA NA KASANCE SHUGABANSA, TO, ALIYU SHUGABANSA .‘’

A riwayar Abu Huraira kuma yace, ta sauka ne ranar 18 ga Zul-Hijjah .

(Tafsir Ibn Kasir, J:2, SH:17)

Idan mu kayi la'akari da wadannan hadisai biyu za muce suna tabbatar mana ne cewa ranar 18 ga Zul-Hijja ne aka cika mana addininmu da wilayar Imam Ali (A.S ), domin ranar ce yayi khudubar qarshe a rayuwarsa (S ), sai dai anyi qoqarin lullube wannan gaskiyar da ba za ta lullubu ba har abada.

So ake a gamsar da mutane cewa ranar Hajji babba aka saukar da ayar don a qaryata wasiyyar Ghadir, alhali littafan sunnah sun tabbatar .

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

Alamis, 11th June, 2020/ 21-10-1441.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post