Rawar Da Malamai Ke Takawa Wajen Jefa Qasa Cikin Bala'i!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED .

YIN KOYINSU GA MALAMAN BANU ISRA'ILA

A duk inda al'umma ta shiga ko ta fada cikin musifa/bala'i akan juyar da al'amarin ne zuwa ga maluma don neman samun mafita, domin sune masana kuma wadanda Allah ya bayyana su a matsayin masu tsoronsa.

Malamai sun kasance masu daraja cikin al'umma ta yadda ba dama abu ya gudana ba tare dasu ba. Wannan dalili yasa duk abinda za ayi dole sai an sanya su ciki domin sune masu tunani da hangen nesa da kuma fada a ji cikin al'umma .

Mulkin siyasa ne ko mulkin gargajiya dole sai an sanyo su ciki don sanin muhimmancinsu. Wannan na nuna mana kenan suna da dama suyi magana in har suka ga ana aikata mummuna daga talaka ne ko hukuma, amma sai ya kasance ba su yin hani kan zaluncin da azzaluman shugabanni ke yi. Idan ka ji suna magana kan wani aikin barna , to, talakawa raunana ne masu aikatawa .

Manzon Allah (S.A.W.W )na cewa;

‘’ Lalle Allah ba ya azabtar da jama'a sakamakon (mummunan aikin )tsiraru daga cikinsu, har sai in sunga (ana aikata )mummuna a tsakaninsu kuma suna da ikon (fitowa )su qyamace shi amma ba za suyi hakan ba(don tsoro ko kwadayi ), to, idan suka aikata hakan sai Allah ya azabtar da kebantattun (masu aikata laifi )da jama'a(da ba su aikata komai ba ).‘’

(MUSNAD, J:4, SH:192)

To, irin wadannan malamai kafirai ne kamar yadda Allah ya tabbatar cikin littafinsa mai tsarki .

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ An tsinewa wadanda suka kafirta daga Banu Isra'ila bisa harshen Dawuda da Isah dan Maryama , hakan kuwa ta faru ne sakamakon sabon da suke aikatawa kuma suna qetare iyaka (ta'addanci).

Sun kasance ba sa yin hani game da mummuna da suke aikatawa (a tsakaninsu ), to, tir da abinda suka kasance suna aikatawa (na rashin yin hani game da mummuna ).‘’

(MA'IDA, AYA TA 78-79)

To, duk wata musifa da kuke gani wacce ke addaban qasa sakamakon miyagun malamai ne.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post