Ranar Uba (Father's Day) Ta Duniya!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

RANAR DA YA KAMATA MU TUNA DA 'YA'YAN SHAHIDANMU

Duk da cewa a wannan harka Islamiyyah akwai ranar da muka ware don tunawa da shahidai(YAUMU SHUHADAH )a wannan qasa, ya kama mubi sahun tuna wannan rana ta duniya .

A wannan rana ce 21th June aka ware me sunan (RANAR UBA ) don tunawa da da Uba ga 'ya'yansu.

Rana ce da kowa ke tuna ubansa yana yi masa kauta ko tunawa da shi in ya rasu.

ME YA KAMATA KA YIWA 'YA'YAN SHAHIDANMU?

Ko ba komai akwai buqatar mubi sahu wajen rana wannan rana ta hanyar tunawa da 'ya'yan shahidai tunda yin haka bai saba koyarwar addini ba.

Mu kasance tamkar mune ubannin 'ya'yan shahidai wadanda ganinmu zai sanyaya musu rai tamkar suna tare da mahaifansu.

Kowanne yaro na nuna qaunarsa ga mahaifinsa ta kowacce fuska da za ta nuna cewa yana da uba, shima yana nuna qaunarsa ga dansa don ya ji cewa shima yana da uba . To, su wadannan 'ya'yan shahidai za suyi baqin ciki na nashin ganin ubanninsu tare dasu sakamakon kashe su da azzalumar hukuma tayi.

Ko ba ayi musu wani abu da sunan tallafi ko kyautatawa a jimlance ba, wato (AMM ), ya kamata a daidaikunmu muyi musu wani abu na kyautatawa wanda zai farranta musu rai har suji tamkar mu ubanninsu ne, wannan zai dadada musu tare da faranta musu rai.

Manzon Allah (S.A.W.W )na cewa;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ NI DA MAI TAIMAKON MARAYA KAMAR HAKA MUKE (ya gwama 'yan yatsunsa biyu ).‘’

Wannan dai ankararwa ce don kada mu gafala da sanya 'ya'yan shahidai cikin 'ya'yan da ke murnar wannan rana na cewa suna da ubanni!

HAPPY FATHER'S DAY 🌳🌾🌺🌷🌿🌹☘️🌲


👨‍👧👩‍👧‍👧👨‍👨‍👧‍👦👩‍👧🏇🏼✋🏼👳🏻‍♂️👳🏾‍♀️

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

21ST JUNE, 2020

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post