@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A bayyane in ana maganar karatu a wannan zamani zai muce cigaba aka samu in mun kwatanta shi da zamunan da suka gabata. Karatun zamani dana addini ya yawaita, sai dai munanan ayyukan jama'a qaruwa yake yi maimakon ya ragu.
Yawan karatun nasu bai bambanta su dana baya ba in batun cigaba ne wajen neman kusaci ga Allah. Za ka tarar wadanda ake kira malamai amma bin son zuciya ya mamaye zukatansu ta yadda ba za su daba bin gaskiya ba.
Wannan al'amari da ban tsoro yake, domin za kaga a kullum dada nisantar Allah ake yi maimakon a qara kusantar Sa. Hakan kuwa na da alaqa ne da manya-mayan alamomin tashin alqiyama da Annabi (S.A.W.W )ya ambata .
Ya zo cikin wani hadisi da ake bayani game da bayyanar fitina a doron qasa inda Annabi (S.A.W.W )ke cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ ZAMANIN (tashin alqiyama )NA TA QARATOWA, AYYUKAN (alkhairi )NA TA TAUYEWA, BIN SON ZUCIYA (na qaruwa cikin zukata ), FITINTINU NA QARA BAYYANA, QUNCI (na rayuwa )NA YAWAITA !‘’
Sahabbai suka ce, yaa Ma'aikin Allah , wanne abune haka?
Yace, ‘’ YAWAN KASHE-KASHE !‘’
(Bukhari , hadisi me lamba 7061)
Wannan shine irin halin da ake cikin musamman cikin wannan qasa tamu Nigeria . A tarihin kafuwarta ba a samun kai cikin mummunan yanayi na zalunci, danne haqqen talakawa, babakeri, bin son zuciya da kashe-kashe kamar wannan lokaci ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Laraba, 24th June, 2020.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Tunatarwa