Malam Adamu Ahmad Tsoho Jos |
–Idishia Jos.
Alhamdulillah wannan zuwa da aka yi na ta'aziyya ita Muslima, ta'aziyya ne da gaba dayan mu ya shafa tunda ana tare da ita kuma ita ma tana tare damu, kuma wannan abin zamu ce gaba dayan mu ya shafa sai mu jajantawa junan mu da fatan Allah ya gafarta mata. Mu kuma idan namu tazo Allah ya kyautata namu karshen yasa mu cika da imani.
Abin da zan so nayi mana nasiha musamman ma dai tunda 'yan media ne suka zo wannan ta'aziyya. Alhamdulillah wannan rasuwa na ita Muslima zai kara tabbatar muku ku 'yan media dama wanda ma basu fahimci muhimmanci da tasirin media a rayuwansa yanzu ba. Wannan rasuwa na ita Muslima an sanar da shi a 'yan media wanda yake nine na soma sanarwa kuma bana sanar a media bane na sanar da wakilan media din ne.
Na dan yi rubutu na sanar da 'yan media cewa; "Yanzu Nan Yau Jumma'a Allah Ya Yiwa Muslima Sheikh Adamu Tsoho Jos Rasuwa". Sai na turawa shi -Idishia, sai Aljasawi, sai Jawad sannan akwai wani group na 'yan Rajabiya na yankin nan, ban da su babu wanda na sanar saboda a lokacin babu data a wayana. To, amma abinda zai bada mamaki wannan sako da 'yan media suka dauka suka 'Modify' aka baza harma suka samo hoto suka hada.
Wanda yake ni ban ma san da hoton ba, amma aka yada, sai ya zamo cewa akalla abinda Facebook suka nuna ya reaching mutane Dubu Sittin Da Hudu da Darurruka ( 64,888 ) haka wanda aka sa a shafin Sheikh Adamu Tsoho Jos. To, kaga wannan zai iya nuna ma Tasirin media a wannan zamani da muke ciki. Kuma tun daga wannan lokacin ban san adadin mutane da suka yi ta'aziyya da masu bugowa da masu ta'aziyya. Wayar ta tsyaa Cak! Wasu ma sun dauka na kashe wayan ne, saboda dare da rana wannan na shiga wannan na fita.
Duk wannan bawani abu bane illa tasiri na 'yan media da suka yada, sai ya zamo mutane da yawa sun samu bayani kowa sai yace ya gani a social media, wannan shine ya sanya a yanzu a da ana cewa bangaren gwamnati ta rabu kashe 3, akwai Executive, Judiciary, da legislative, wannan sune ake kira 3 Aims Of Government. To, amma Yanzu sunce Mass Media ta zama daga ciki ya zama 4 Aims Of Government, saboda ta hanyar Mass Media akan iya can za tunani ko canza Gwamnati.
Lallai wannan abinda ya faru na shi wannan sanarwan rasuwan ita Muslima ya bazu ko ina har kasashen waje America, daga England daga Turkiyya, daga China Daga India ma Su Iran Su Iraki su Saudiya ba inda wannan sanarwan bai je ba ba kuma inda ba'a bugo min waya ba dama nan cikin gida Nigeria. Wannan kuna gani yau anyi kwanaki da rasuwan ita Muslima amma har yanzu mutane zuwa suke. Idan ka tambaya a ina suka samu labari ? Social Media daga media ne aka samu labarin.
Dan haka yana da muhimmanci ku fahimci wannan aiki da kuka dauka zakuyi aiki ne wanda yake da girma da lada kuma in anyi shi ta hanyar da ya dace. Domin kamar yadda nake bayani duk adadin wanda suka zo suka yi addu'a nan, dama wanda basu zo ba suka tura 'Text' ko suka gani suka jajanta kuna da sakamako na lada, ko wanne mutum daya kuna da sakamako lada akansa.
Akwai ruwaya cewa idan zaka yi sadaka, misali idan na dauki kudi kamar naira 10 zan yi sadaka sai na bawa -Idishia shima ya bawa Ibraheem duk aka zaga kowanne anan wannan sadakan ya bi hannunsa sai ya zamo Daga karshe aka ba almajiri to dukkan mu nan za'a bashi ladan kamar shine yayi sadaka nan. Ni kuma lada na yana nan, kaga Raguwa akayi ko cigaba? Cigaba ne ! To, kaga media an Isar wannan ma Isar kayi posting wannan ma yayi posting, wannan KUMA yayi Share waccan ma tayi share.
Kullum ina magana a media kada ku dogora ga Liked, amma kasan me zaka yi sharing, share yafi Liked domin idan kayi sharing idan kana da abokanai (100) zasu ga wannan. Suma wata kil idan suka ga amfanin wannan abin zasu share din sa. Sai ya zamo kai ka samu lada kuma shima ya samu ladan abokinsa. Amma shi liked wanda kayi liked din abin shi kawai zai gani, don haka sharing yafi ka liked posting din mutum. Kasan me zaka share hatta liked din ma kasan mai zaka liked a social media, domin in kayi liked mummunan abu ya nuna kana tare da shi in kayi liked kyakkyawan abu ya nuna kana tare da shi. Don haka hatta liked da sauransu sai ya zama muna tantancewa.
Mu na farko mu fahimci muna da hadafi, da aka halicce mu, wanda sauran mutane sun gafala menene manufar rayuwa ! Menene manufar halittan 'dan Adam zuwa Duniya ! Me yasa Allah ya halicce mu zuwa duniya ! Me zamuyi anan duniya ! Bayan duniya mai za'a yu! Idan an mutu mai za'ayi ? To, kaga mu munsan hadafin halittan mu da kawo mu ita wannan doron kasa shine mu bautawa Allah. Allah yana cewa; Allah bai halicci mutum da aljanna ba sai dan su bauta min.
Don haka zai zamo hadafin mu muna rayuwane domin kubutar Allah, muna bautar Allah ne don mu samu yardar Allah. Ba zai zamo hadafin mu kamar sauran mutane ba, suna rayuwa domin ya zamo sun rayu, idan zaka tambayi mutum ina zaka je Neman abinci, ina ka fito Neman abinci kaga ba banbanci da dabba. Allah ya mana baiwa da ni'ima na kasamtuwar mu Almajiran Malam (H)
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN