Me Gwamnatin Jihar Kaduna Da Jami'an Tsaron Ta Ke Nufi Da Almajiran Sayyid Zakzaky Ne??



Tun bayan aika-aikan da Sojojin Najeriya suka aikata a ranar 12 ga watan 12 Shekara ta 2015 a garin Zaria a kan Shaikh Zakzaky da almajiransa, gwamnati ke rike da shi ba tare da laifin komai ba. A yayin da almajiran Shaikh Zakzaky da dukkan masu son adalci suke ta kiraye-kiraye a sake shi, sai ga shi gwamnatin ta fake da cewa: wai tana tuhumar sa da sa mabiyansa kisan kai, alhali mabiyan nasa an yi shari'a da su a gaban kotuna daban-daban, amma sun kasa tabbatar da hakan, don haka kotunan suka sallami almajiran Shaikh din, kamar yadda shi ma babban kotun da ke Abuja ta yi umarni da a sake shi a shekarar 2016.

Mun samu rohotannin sirri a wannan makon da ya gabata cewa, akwai wani yunkuri da gwamnatin jihar Kaduna da jami'an tsaronta ke yi a kan almajiran Sheikh Zakzaky, musamman masu fita muzaharorin lumana na Free Zakzaky.

A wannan lokacin da hankalin duniya ya koma kan Annobar Coronavirus (COVID-19), jami'an tsaro suna so su yi amfani da wannan dama, wajen auka wa almajiran Sheikh Zakzaky na garin Kaduna da kama fitattun 'yan' uwa, musamman masu fita muzaharorin lumana na free Zakzaky da ake yi a duk mako.

Sannan sun dau hayar mutane daga wajen Kaduna, maza da mata, wasu za su kasance a cikin sahu, wasu a wajen sahu, a yayin da na ciki za su yi kokarin canza taken muzaharan, ko su tsokani jami'an tsaro a lokacin da suka zo wucewa. Sannan za su yi amfani da sandar shokin (shocking stick), wajen kama almajiran Sheikh Zakzaky, a yayin muzaharorin.

Don haka muna sanar da Al'umma, Harkar Musulunci karkashin Sheikh Ibrahim Zakzaky, ta barranta daga dukkan wani nau'i na tashin hankali kowane iri. Harkar Musulunci ba ta taba daukar matakin tashin hankali ba a tsawon shekaru sama da 40 na wanzuwar ta. Sanannen abu ne cewa Harkar Musulunci a Najeriya ba ta taba tayar da hankali ba, hatta a lokacin da ake tunzura ta. Wannan kam wani abu ne da ba zai canza ba duk tsananin .tunzurawa.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post