Matsalar Samun Mazajen Aure Ga Ƴaƴa Mata!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

LAIFI NA YARA NE KO NA MAHAIFANSU?

Komai da ka sani yana da mafita cikin addini, sai dai bin son zuciya ya hana mutum gani ko ya hana masa bi.

Ayoyi masu yawa na bayyana ga mutane amma sun kasa daukar darasi saboda son duniya da qyalqyalinta ya rufe musu ido.

Mata sun yawaita a wannan zamani, suna buqatar aure amma sun kasa yi, wasu laifinsu ne wasu kuma laifin iyayensu ne.

Buri da kwadayi yayi naso cikin zukatansu, ana karantar dasu addini amma ba sa aiki da wannan karantarwa. Da ace za suyi aiki da abinda ake fada musu, to, da za a sami sauqi cikin al'amarin.

Addini da dabi'a sune madubin da ake dubawa wajen neman mace ko mijin aure, amma a yanzu dukiya ita ce madubi. Kuma duk wanda yace dukiya ce madubinsa, to, lalle ba zai ga mai kyau ba, domin ita ce musabbabin halaka.

Manzon Allah (S.A.W.W )na cewa;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ IDAN WANDA KUKA YARDA DA ADDININSA DA 'DABI'UNSA YAZO MUKU (don neman aure ), TO, KU AURAR MASA. IDAN KUWA BA KU AIKATA SHI BA, FITINTINU ZA SU KASANCE , KUMA FASADI (na yin cikin shege da zubar da shi )ZAI BIJIRO.‘’

Suka ce, yaa Ma'aikin Allah !Ko da ya kasance tare da shi akwai ....(basu qarasa maganar ba sai ya katse su da cewa ),

‘’ IN DAI HAR WANDA KUKA YARDA DA ADDININSA DA 'DABI'UNSA YAZO MUKU, TO, KU AURAR MASA.‘’

Sau uku yana fadar haka.

-Sunan Abu Dawud, J:4, SH:205.

-Tuhfatul-Ahwaaz na Tirmidhi , J:4, SH:204.

Amma duk da haka sai kaga mutumin kirki ma'abocin addini yazo neman aure, amma idan shigarsa ta nuna mabuqaci ne ba mawadaci ba, sai kaji ana cewa anyi mata miji ko ace karatu za tayi.

To, shin wannan laifin na wanene ?

Tare da Ado Isah Guda.

          09039791509

Litinin, 15th June, 2020/ 25-10-1441.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post