kun zama Summun Bukumun Umuyun(wato kun kurumce kun bebance kuma kun makafce bakuji Baku gani) duk da sunan wai ku masoya shugaba buhari ne.
Bakuso a fadamasa gaskiyar lamarin da kasa take ciki don ya gyara, ko Allah yasa yayi nasara ta yadda zai tsira da mutuncinsa. Wai kuma kune masoya buhari, MASOYA KO KUMA MASU SOYA BUHARI??
kalli yadda tsaro ya tabarbare a jahar katsina mahaifar shugaban kasa, kullum abin sai gaba yake ba sauki ciwon arne, amma da anyi magana sai MASU SOYA BUHARI, suyo caaaa! Wai ana adawa.
Kalli yadda shinkafar gida take naira dubu goma sha takwas buhu, kalli buhun masara dubu sha hudu buhun gero dubu sha biyar, kuma babu hanyar samun kudin amma da anyi magana sai kaji makaffin cikin mu suna cewa tattalin arziki ya inganta wai an tara foreign reserve (kudin ajiya na kasashen waje) Hmmmm! Ina amfanin badi ba rai.
Don Allah MASU SOYA BUHARI, kubar MASOYA BUHARI na gaskiya su fadamasa gaskiyar lamarin da kasa ke ciki ko Allah yasa ya farga ya gyara domin ya tsira da mutuncin sa.
TO! KO BA MAGANA DAI A ZURA IDO TA ISHI MAI HANKALI, GA YADDA TA KAYA NAN A GARIN YAN TUMAKI NA JAHAR KATSINA A JIYA INDA AKA RIKA KONA HOTON BUHARI DA MASARI.
MUSA IBRAHIM DAURA
10-6-2020.
Tags:
Daga marubata