Ita Ƙasar Nan Faɗa Da Allah Ake Yi Kai Tsaye – Sheikh Yakub Yahaya Katsina



"...To inda abin ma yafi muni ba ma ana kashe humanity bane a'a ana ma faɗa da Allah ne (Nijeriya ana faɗa da Allah ne).
Ƴan bokon (Gwamnatin) Najeriya basu da abokin faɗa sai Allah, toh! Wanda yace; zai yi faɗaa da karatun Al'ƙur'ani ai yana faɗa da Allah ne. Sai aka fake da hana bara dan a hana karatun Al'ƙur'ani, ai kunji ana maganar hana bara ko? “Ana cewa ai wanene mabarata… wanene… yara basu zuwa makaranta ‘out of school' wadanda basu zuwa Makaranta sun kai miliyan goma…” kuma dukkan su waɗannan yaran ko suna Makarantar Allo suna yin rubutu, suna yin karatu dole su tafi makarantar boko ko duk a ce masu jahilai saboda basu yin rubutu daga hagu zuwa dama.

Bamu ce kar ayi rubutu haggu zuwa dama ba…abinda muke so a fahimta; shi ilimi akan yi shi ne dan a amfani kai, Kai ka afani kanka, ka amfanar da wasu. Ilimin boko in anyi, in ka zama malamin lafiya zaka amfani kanka zaka amfani al'umma, in ka zama malamin al'amuran ruwa zaka amfani kanka zaka amfani al'umma, in ruwa ya kakare ko aka rasa ruwa kai za a nemo ka taimaki mutane su samu ruwa… haka wutar lantarki in ya tsaya kai ne za a nemo in kai ma'abocin wutar lantarki ne mutane su samu hasken wutar lantarki…

To Ilimin nan na Al'ƙur'ani da al'umma take yi yau shekara kusan 900 yana da amfani ko baya da amfani?

 Yana hidima ga al'umma ko baya yi?

 Yanzu idan za ayi sallar juma'a Shaikh ne ko kwamishina ne zai shiga gaba?

Wa ke shiga gaba ya ja sallah? (Amsa) liman ne, to shi wannan liman din daga Makarantar Allo ya fito sai da yayi Makarantar Allo sannan yayi ta zaure, kila sannan yaje jami'a ya zama furofesa ko Dakta ko wani abun.

To idan aka ce ga jana'iza ta faru ana so ayi ma wannan gawar sallah wa zai yi sallan? Idan za a ɗaura aure, idan ana son roƙon ruwa, idan bala'I ya sauko, duk wa ke wucewa gaba? Shi ne Malam. Mi ake karantawa? Al’ƙur’ani da Addu'o'in da suka gangaro daga Al'ƙur'anin ba jarida ake karantawa ba...

Ba wani gwamnan da ya hau kujera sai da yaga Malam yayi masa addu'a, ba wani ciyaman ko sakatare kai hatta ma wadanda ba Musulmi ba, sukan je wajan Malamai suna rokon ayin masu addu’a.

 Indai wannan ilimin na da amfani irin haka to ya kamata a mutuntashi ba a rusa shi ba kuma ya kamata ma idan akayi bajat na ma'aikatar Ilimi sai a raba gida biyu, wannan na wadannan ne wannan na wadannan ne, tunda duk mun yarda yana da amfani ga Al’umma. Ita wannan al'ummar wannan ilimin ta zaɓa kuma ta ke so tayi kuma ta amfani kanta duniya da lahira, in anje lahira ma dashi ake magana.

Wancan kuwa shi na sana'a ne da inganta rayuwar duniya “WANDA ALLAH YA BA DUBARA YAYI AMFANI DA WANNAN ILIMIN YA CI RIBAR DUNIYA DA LAHIRA..."

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post