Ina Kuke Masu Suna Fatima, Ku Saurari Wannan!!!






Tare da *Salisu Umar Mazajen Zakzakyya*

Da farko kafin komai ga dan wani labari saiku saurara 👇
Anyi wani magidanci wanda ya kasance yayi aure-aure, to a cikin aure-auren nan nasa sai Allah ya hadashi da wata mata mai suna FATIMA!
Ita wannan fatimar ta kasance macece kamula mai riko da addini gata da sanin duk wani hakki na aure, bata zamanto mai yawan zama a cikin sauran mata don yawan hira da 'yan gulmace-gulmace ba kamar yanda yake gudana a tsakankanin wasu matan ba.
Fatima macece tagari daga cikin dabi'un fatima a duk ranar da ba a dakinta zai kwana ba kullum tana muhallinta batta da aiki sai ibada karatun qur'ani salloli da zikirori.
Duk ranar da ya zamto ranar kwananta ne kuwa tana ajjiye dukkan wata hidimatata ya zamto aikinta shine na mijinta, daga cikin dabi'arta shine duk lkcn da mai gidanta ya fita ya dawo gida zai tarar da ita a bakin zauren kofar gida tana jiransa, zata tarbeshi cikin kulawa da soyayya, zata kasance cikin bashi kulawa har lkcn da zai gama kwanansa a dakinta, an tambayi wannan magidancin yake cewa "Fatima idan ta kwanta barci bata juyi na kwanciya saita nemi izininsa sbd gudan karta saba masa!
Sanadiyyar fatima ya zamto baya tunani ko sha'awar kara auren wata mata.
Shin ko kunsan miya faru dashi a wannan lokacin? Allah ya karbi masoyiyarsa wacce yafi so wato Allah ya yiwa Fatima rasuwa! 😓
Rasuwar fatima ta zautar dashi yayi kuka marar adadi 😥 a karshe bai yarda ankai gawar matarsa makabarta ba a gidansa yayi mata kabari, a wannan yanayin sai ya zamto ko ta'aziyya ba a zuwa masa don kana masa ta'aziyya zai fashe da kuka 😥
Hmmmmm Allah mai iko a wannan yanayin sai Allah ya jarabce shi da son duk wata mai suna Fatima, cikin ikon Allah sai ya sake auren wata Fatima!
Hmm ko kunsan miya faru? An saba number Fatimar da ya aura batacu sunantaba tunda ta shigo bai sake samun kwanciyar hankali ba ta zamto masa kamar wuta, suna cikin wannan yanayi wata rana wannan Fatimar ta tayar da rikici da uwar gidansa. A lokacin uwar gida ranta ya baci ta zabura cikin zafin murya tace " kedai bakiyi halin Fatima ba mun zauna da Fatima" cikin zafin murya ta zabura tace "kedai Wallahi kabarin Fatima ma ya fiki!" Ta fadi haka sai a kunnen mijinta take ya zabura yace "kwaraiiii kuwa!"
Anan ya rabu da wannan Fatimar, wata rana ana tambayarsa yace "akwai abunda yake tunowa yayi kukaa😥 wata rana Fatima tana kwance a bari daya hakarkarinta ya gaji ta nemi izininsa zata juya yace aa, ranar a haka takwana! Sbd hk duk lokacin daya tuno sai yayi kuka 😥
TUNATARWA
Shin 'Yar uwa me zai hana kiyi koyi fa fatima ta farko?
Shin kina tunanin kasan cewarki mai suna fatima ba wata karramawa bace?
Wannan misali bai takaita akan mace mai suna fatima kadai ba! Sannan labarinnan gaskiyane ya faru
Assalatu was salamu aliki ya bintu Muhammadur rasulullah (sa)

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post