@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TSORO DA KWADAYI KATANGA CE TA HANA FADAR GASKIYA
Na taba ji daga bakin wani malami a garin Bauchi me suna USTAS IDRIS ABDUL-AZEEZ DUTSEN TANSHI yana CEW;
‘’ MUTUM BA ZAI IYA FATAR GASKIYA GA AZZALUMI BA HAR SAI YA HADA ABUBUWA 3;
-RASHIN TSORO,
-RASHIN KWADAYI DA KUMA
-JARUNTA ·
Tabbas maganarsa haka take, domin tsoro ba zai barka ka fadawa azzulumar hukuma gaskiya ba , haka ma kwadayi ba zai barka ba don kada ka rasa na qashin miya · Sannan idan kai ba jarumi bane da zarar ka fadi gaskiya kuma aka kira ka aka tsoratar da kai ta hanyar barazana , to, kana dawowa za ka canza magana kamar shehu mai kwatance (na Jos ).
Jin tsoro ba zai zama uzuri gare ka wajen Allah ba, domin idan ya kasance tsoron zai hanaka fadar gaskiya, to, saqon Allah ba zai isa kamar yadda yace a isar dashi ba.
Ya zo cikin wani hadisi daga Manzon Allah (S·A.W.W )yana cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ Kada dayanku ya cutar da kansa ta hanyar ganin wani al'amarin Allah (da ya kamata ace wani abu a kansa )amma ba zai ce komai a kansa ba· Har ranar alqiyama ace masa;
‘’ ME YA HANAKA KA KASANCE KA CE (wani abu )CIKIN KAZA-DA-KAZA-DA-KAZA ?‘’ Sai yace ,
‘’ Tsoron mutane ne (ya hanani fadar gaskiya )·‘’ Sai (Allah )yace;
‘’ AI GARE NI YA FI CANCANTA DA KA JI TSORONA (don ni nake da wuta da aljannah ).‘’
-Sunan Ibn Majah , J:2, SH:1328, Hadisi me lamba 2008.
-Musnad Ahmad, J:3, SH:73
TO, BISA WACCE HUJJA CE ZA KA KASA FADIN GASKIYA ?
Daga wakilanmu na Bauchi zone ·
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Laraba, 10th june, 2020/ 20-10-1441.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN