Hanyar Taimakon Azzalumi Kala Biyu Ce!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KUYI TAIMAKEKENIYA KAN AIKIN ALKHAIRI DA TAQAWA

A duk inda ka ji an ambaci kalmar zalunci sai ka ji kalmar ba ta da dadin ji, ko da kuwa ba a taba zaluntarka ba matuqar kai mumini ne.

Ita hanyar taimakon azzalumi kala biyu ce kamar yadda muka ambata a sama, sai dai dayar mummuniya ce, dayar kuma wacce aka yi mana umarnin aikatata .

Hanyar farko ita ce taimakon azzalumi kan aikata zaluncinsa, za ta iya kasancewa ta hanyar goya masa baya ne a furuci, rubutu ko kuma a aikace ta yadda zai ji dadin cigaba da aikata zaluncinsa, to, ita wannan hanya ta kasance mummuniya .

Hanya ta biyu kuma ita ce wacce Anas Bn Malik ya kawo daga Manzon Allah (S.A.W.W )yana cewa;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ Ka taimaki dan'uwanka azzalumi ko wanda aka zalunta.‘’

Aka ce , yaa Ma'aikin Allah, wannan dai za mu taimake shi don wanda aka zalunta ne, amma ta yaya za mu taimaki shi in har ya kasance azzalumi ? Yace;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ Ku gajiyar da shi (ta kowacce hanya yadda ba zai aikata ba ), kuma ku hana shi daga aikata zalunci (ta kowacce fuska ), to, wannan shine taimakonsa.‘’

(Bukhari , J:3, SH:168)

Idan kayi iya qoqarinka ka hana mutum aikata zalunci , to, ka taimake shi ta hanyar kare shi daga shiga wuta. Wannan hadisi ya zo daidai da ayar nan dake cewa;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ KUYI TAIMAKEKENIYA AKAN AIKIN ALKHAIRI DA TAQAWA, KUMA KADA KUYI TAIMAKEKENIYA AKAN ZUNUBI DA ZALUNCI ."

(Ma'ida, aya ta 2)

Kunga anan za mu iya fahintar cewa yin shiru ma na daga cikin taimakonsa ta bayan gida, domin yin shiru yarda ne.

Allah yasa mu dace.

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

Laraba, 10th June, 2020/ -20-10-1441.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post