Gyara Baya Yiwuwa Sai Ansha Wahala!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DOLE A YIWA BABA BUHARI UZURI

Al'ummar wannan qasa tamu Nigeria ta shafe shekaru goma sha shida (16) qarqashin mulkin PDP ta kai har aka qosa da mulkinta don ana neman canji.

Duk da cewa anyi walwala ta bangaren tattalin arziqi lokacin gwamnatin Obasanjo, domin lokacin ana cikin tsari na bawa qananan hukumomi (L.G )gashin kansu wadanda suka fi kusa da talakawa, amma a qarshen rugujewarta an fada matsakar boko haram.

Tun daga wannan lokaci aka gano cewa mulkin da arna suke yi ne ya jawo wannan al'amari, saboda haka aka kada gangar kira ga jihadi don share wadannan arna .

Kashi 65% na al'ummar wannan qasa suka ga babu wani mutumin kirki mai imani da tausayi kamar baba Buhari , kuma musulmi . Saboda haka suka bada rayukansu da dukiyoyinsu da lokacinsu don ganin ya hau kan karagar juya Nigeria .

Dama kunce yafi kowa tunani, saboda haka cikin tunaninsa ya nuna mana cewa gyara fa sai an sha wuya, kuma ya nuna mana cewa akwai wasu mutane cikin iyayenmu da yayunmu da 'ya'yanmu da qannenmu da suka kasance barana ga tattalin arziqin qasa, saboda haka ya dau matakin karkashe su don samar da walwala.

Ya umarce mu da komawa gona don bunqasa arziqin qasa, kuma ya tsare bododi don inganta nomanmu da kiwonmu, duk da cewa bai sami ikon bamu taki ba.

Ya daga mana farashin man fetur don arziqin qasa ya qaru domin shi masanin tattalin arziqin qasa ne.

Cikin hikima irin tasa ya karbo mana kwangilar Covid-19 don mu sami tallafi daga qasashen waje, hakane, duk da cewa an shiga qunci na rayuwa da rashin 'yancin aikata addini, amma ai gyara ake yi wanda ba ya samuwa har sai an sha wuya .

Don kana sayen mudun shinkafar gida #450, dawa #200, wake #200 bai kamata kayi butulci ta hanyar zaginsa ba, domin gyara ba ya yiwuwa cikin sauqi.

AI ALQARI YA 'DAUKA ZAI GYARA NIGERIA , KO KUNGA YA SAUKA NE BAI GYARATA BA?

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

17th June, 2020/

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post