Gwamnatin Da Take Kashe Ƴan Shi'a Kuke Ta Murna, Ita Ce Dai Take Ta Kashe Ku A Kullum




🇳🇬 Ma'asumah Hausa Nigerian News Updates

Tare da Muhammad Aliyu Daud (Dansudan) Azare 070-32803940

  Su 'yan shi'a suna zuwa musu da " "Uniform" dinsu su kashe su haka kawai, basu dauke da makami! *Sabida sun san cewa in suka zo babu "Uniform" zamu kamasu ne, mu tona asirinsu kamar yadda muka kama wanda yazo cikinmu da "Bom"*

  Su kuma mutanen Gari sai suke yi musu badda kama, suke zuwa musu babu "Uniform" da wasu sunannaki na munafurci kamar ace maka 'Barayin Shanu, Makiyaya, Masu Garkuwa da Mutane, Boko Haram da sauransu! Suke kashe mutane haka kawai. *Sun kashe 'yan shi'a da "uniform" sun kashe mutanen Gari babu "Uniform" ta hanyar radawa kansu suna, Barayin shanu ko Makiyaya, ko Boko Haram*

  Harma tazo ta bayyana lokuta ma banbanta Da "Uniform dinma suna kashe mutane, da "Uniform" din ajikinsu su kashe mutanen! Wanda hakan ya nuna ma sune masu kisan.

 Amman sun raba kanmu suna cutar damu! *Sun fara da 'Yan Shi'a sabida suna qira adawo ayi adalci! Ayi hukunci da Littafin Adalci wato Qur'ani. Shine suka fara dasu sabida sunsan cewa, su suna qirane zuwa ga adalci kuma bazasu taba zura ido suga ana zalunci su yi shiru ba!*

 Wannan anga misalin 'yanda suke temakawa wanda aka zalunta, a wajaje mabanbanta!

 *Tabbas Gwamnati ce take yin wannan kisan! Inba haka ba ta tsai da kisan mana!*

 Ta iya tura jami'ai dubu (30,000) talatin sabida zabe amman bata iya kare rayukan talakawa ba!

 Ta iya kare rayuwar shinkafa 'yar Qasar waje kada talaka ya sayi shinkafa ta qasar waje! Amman bata iya kare rayukan talakawa ba!

 Maharan da yake sune suke yin kisan! Da shinan Gwamnatin sukan share fiye da awa Goma suna kisa, hankalinsu kwance! Baza kaji an tura musu jami'ai ba!
 Da yake sune suke kisan!

 Wannan Malamin nan da suka farwa sabida su kashe don fadan gaskiyar sa, ba tare dajin tsoron kowa ba! Sabida yanda yake son talakawa da zaman lafiya! Da ci gaban Qasar gabaki daya!

 Ya fito ya fada mana tuntuni cewa Gwamnati ne Bokoharam! Kuma basu qaryata ba, basu kuma kai shi qarar ba (Kotu)! Sun san cewa gaskiya ya fada!
 Kuma kowa yaji a lokacin Jonathan, Jonathan yace;- "a cikin Gwamnati akwai 'yan Bokoharam"
 Wanda fassarar hakan shine Gwamnati ce Bokoharam! Ita take basu makamai da abinci da komi!

 Wani masanin al'amuran yau da kullum yace "Duk wani matsala da take faruwa a qasa, ya wuce awa 24 ba a yi maganinta ba, toh da hanun Gwamnati a ciki"

 Wannan ya qara tabbatar mana da cewa duk wannan kashe-kashen da ake yi Gwamnati ne take yi!

 Toh shi wannan ba iya awa 24 da ya ci ba, a'a maganar shekaru ake sama da shekaru Goma (10).

 Ba zuba ido zamu yi ba mu tashi mu nemi 'yancinmu, kun gani da iya Borno ne da kewayenta! Amman yanzu ya Shiga Zamfara da Katsina da Sokoto. Toh kaima wallahi inka tsaya zuba ido zai iso wajenka, don wallahi ba tsira ka yi ba!

 Mafita itace mu tashi mu kwaci 'yancinmu kafin lokaci ya qure mana! A mayar da qasarmu kamar Somaliya ko Iraqi ko Siriya!

 Mu amsawa qiran wannan bawan Allah Sheak Zakzaky! Mafita tana hanunsa! Qiransa na adalci ne da zaman lafiya!


*FREE ZAKZAKY WA UMMUH ZEENAH*

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post