@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HAR SUMBATUN SHIGA 'DAKINTA YAKE A HALIN JINYAR DA YAYI WAFATI
Da gaske ne Allah (T )ya fifita sashen Manzanni kan sashen , ‘’ TILKAL RUSULU FADDALNAH BA'ADHUHUM ALAH BA'ADHIN...‘’.
Haka zalika yake fifita wasu bayinsa kan wasu don matsayinsu a gurinsa.
Ummul-muminina A'isha na daya daga cikin matan Annabi (S.A.W.W )data zauna da sauran matansa in ka cire Sayyyidah Khadijah (S.A ).
Duk maganar da za muyi bai shafe ta ba, domin kuwa bata zauna da ko daya daga cikinsu ba.
Bukhari ya riwaito cewa, Ubaidullahi Bn Isma'il ya bamu labari, baban Usamata ya bamu labari daga Hisham, daga babansa cewa, Manzon Allah (S.A.W.W )ya kasance yana kekkewayawa a tsakanin matansa yayin da yake cikin halin rashin lafiyarsa yana cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ GOBE A INA NAKE ? GOBE A INA NAKE ?‘’
Kawai kwadayinsa shine shiga dakin A'isha (in ji mai bada labarin ). A'isha tace,
‘’ AMMA IN HAR YA KASANCE A RANATA CE SAI YAYI ZAMANSA (ba ka qara jin yana tambayar dakin wa zai koma gobe ).‘’
-Bukhari , hadisi mai lamba 3774.
DARASI
Wannan hadisi na nuna mana ne tsantsar irin soyayyar da Annabi (S .A.W.W )ke nuna mata, kuma dukkan aikinsa abin koyi ne.
Gare ku masu mata 2, 3, ko 4.
Ya kamata ka riqa bayyanar da so ga wacce kafi sonta cikin matanka ta yadda kowa zai fahinci haka har a riqa bada labari a waje.
Yin hakan zai zama dabbaqa sunnah .
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH .
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Talata, 16th June, 2020/ 26-10-1441.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN