@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
'YAN'UWANTA SUN KOKA KAN IRIN ABINDA SUKE GANI
Babu mai musu kan cewa akan nemi yardar mutum ko farranta masa rai ne ta bin hanyar da aka ga ya fi juya akalarsa. Shi yasa za kaga wasu sukan bi ta hanyar matar mutum nevin suna son wani abin hannunsa ko neman shiga jikinsa.
Wataqila hakan na da alaqa ne da ganin yadda Sahabban Annabi (S.A.W.W )ke yin kyautarsu ga Annabi (S.A.W.W )yayin da suka san yana dakin Ummul muminina A'isha.
Ba a kawo dai hanyar da suke gane hakan ba, domin matansa (S )sun kai goma (10).
Shin, shi yake sanar dasu cewa yau a dakinta yake ko kuma dai su suke lura da shi har su gane? Ba a dai kawo ba, amma dai su suna sani.
Bukhari ya riwaito cewa, Abdullahi Bn Abdulwahab ya bamu labari, Hammad ya namu labari, Hishaam ya bamu labari daga babansa yace;
‘’ Mutane sun kasance suna kirdadon yin kyautarsu ga Annabi (S.A.W.W )a ranar A'isha . Sai 'yan'uwanta (kishiyoyinta )suka taru zuwa ga Ummus-Salama suka ce;
‘’ YAA UMMU SALAMA, WALLAHI MUTANE FA SUNA KIRDADON YIN KYAUTARSU GA ANNABI NE A RANAR DA YAKE 'DAKIN A'ISHA. AI MUMA MUNA FATAN ALKHAIRI KAMAR YADDA A'ISHA KE FATANSA . KI FADAWA MANZON ALLAH (S.A.W.W )YA UMARCI MUTANE DA SU RIQA YI MASA KYAUTA A DUK INDA YAKE, KO A DUK INDA YA JUYA .‘’
Tace, sai Ummu Salama ta fadawa Annabi (S.A.W.W). Tace,
‘’ SAI YA KAWAR DA KANSA DAGA GARE NI. A YAYIN DA YA QARA JUYOWA GARE NI SAI NA TUNA MASA MAGANAR, SAI YA QARA KAWAR DA KANSA DAGA GARE NI. A KARO NA UKU DANA QARA FADA MASA SAI YACE;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ YAA UMMU SALAMA ! KADA FA KU CUTAR DANI CIKIN AL'AMARIN A'ISHA , DOMIN WALLAHI WAHAYI BA YA SAUKO MIN YAYIN DA NAKE SHIMFIDAR 'DAYA DAGA CIKINKU IN BA ITA BA !‘’
(Bukhari , hadisi me lamba 3775)
Saboda haka bai kamata mata su riqa nuna wata damuwa ba don sunga abokan mijinsu na yawaita zuwa wajen mijinsu a ranar wata daga cikinsu, sai dai in koyi za suyi da su Ummu Salama (R.A ), amma za su iya fuskantar qalubale daga mijin nasu.
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Laraba, 17th June, 2020/ 27-10-1441
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN