Fifikon Ummul Muminina A'isha Akan Sauran Matan Annabi (S.A.W.W) !!!(3)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ITA TAFI KOWA KAMALA CIKIN MATAN AL'UMMAR MANZON ALLAH (S.A.W.W )

Cigaba:-

Duk abinda ya fito tabbatacce daga Manzon Allah (S.A.W.W ), to, yin shakku ko jin wani qeqayi cikin zuciya kafirce ne, domin shi ba ya magana bisa son zuciyarsa , sannan abinda kaji ya fada wahayi ne.

Sanin halin wadanda ya rayu dasu yasa ya gargade su kan cewa duk wanda yayi masa qarya ya tanadi masaukinsa a wuta .

Ya tabbata cikin sahihul Bukhari cewa babu kammalalliyar mace cikin matan al'ummar Manzon Allah (S.A.W.W )in har ka cire Ummul muminina A'isha, wanda hakan ke nuna cewa ita ce mafificiyar matan talikai, domin al'ummar Annabi (S )ita tafi kowacce al'umma daraja.

Daga Bukhari yace, Adamu ya bamu labari yace, Amru ya bamu labari , Shu'ubatu ya bamu labari daga Amru Bn Murrata , daga Murrata, daga Abu Musa Al-Ash'ariy yace;Manzon Allah (S.A.W.W )yace;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ DA YAWA DAGA CIKIN MAZAJE SUN KAMMALA , AMMA BABU WADANDA SUKA KAMMALA DAGA MATA SAI MARYAM 'YAR IMRANA DA ASIYA MATAR FIR'AUNA . KUMA FIFIKON A'ISHA AKAN MATA TAMKAR THAREED (wani kalan abinci )NE AKAN SAURAN ABINCI .‘’

(Bukhari , hadisi me lamba 3769)

            SHARHI
         ――――――

Qur'ani ya ambaci Sayyidah Maryam da kuma Asiya da kyakkyawan ambaton da babu mai inkarin kamalarsu .

Na'am, Qur'ani ma ya kawo maganar matan Annabi (S.A.W.W ), sai dai bisa sigar zargi ne ba ambaton yabo ba.

‘’ WA'IN TAZAAHARAH ALAIHI FA INNAL-LAHA HUWA MAULAHU....‘’

Sannan ambaton ummul muminina da wannan fifiko na kore kamalar Sayyidah Fatimah (S.A )ne, alhali ita har ayar tsarkaka ce ma ta sauka a kanta, amma wannan hadisi na nuna akwai wacce tafi tsarkakakkun da Allah ya tsarkake.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

Alamis, 18th June, 2020/ 28-10-1441.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post