—Yau da gobe bata bar komai ba, 'Yan Arewa a mulkin Buhari.
====================
Kada ka zamo mai goyon bayan Azzalumai, a koda yaushe ka zamo mai son Adalci. Kuma kar ka zamo mai yin shiru da bakinsa a duk lokacin da kaga ana zaluntar wani (koda kanada bambancin ra'ayi ko fahimta tsakaninka da shi) domin kaima wata rana Azzaluman da suke muzguna masa zasu iya zuwa ta kanka. Shi zalunci; ko kai akewa yiwa ko ba kai ake yiwa ba; sunanshi Zalunci, kuma be kamata ka goyi bayanshi ba.
A lokacin da Buhari ya Kashe muna 'yan uwa a Zariya kuma ya kama Malaminmu ya daure tun a wancan lokacin har yanzu da nike wannan rubutu ba tare da ya aikata laifin komai ba; Saboda makauniyar soyayyar da 'yan Arewa suke yiwa shugaba Buhari, idan muka ce Buhari ya Zaluncemu; sai kaji suna jifarmu da kalamai marasa dadin ji, wasu suce karya ne, wasu kaji suna cewa Allah ya kara (Suna yimuna dariya), kai akwai ma wa'enda suka daina gaisawa damu saboda muna cewa Buhari ya Zaluncemu, wasu kuma sun yarda an zaluncemu din amma soyayyar Buhari ta hanasu su fadawa duniya cewa lallai an zaluncemu. 'Yan kadan ne daga mutanen Arewa suka nuna rashin jin dadinsu akan abunda Buhari ya yi muna.
Tun daga wancan lokacin duk da cewa akwai matsalar harakokin tsaro a yankin arewa maso gabas amma babu tsiyar da Shugaba Buhari ya tsinanawa Mutanen Arewa har wa'adin mulkinsa na farko ya kare, suka rika cewa; “Ai yanzu da an koma Nexlevel Baba akan arewa zai maida hankali”. Sai gashi Buharin ya koma a karo na biyu amma lamura sai kara lalacewa suke yi, matsaloli karuwa kawai suke yi, tun daga rikicin Boko haram (a Arewa maso gabas), Masu garkuwa da mutane (a Arewa ta tsakiya) da rikicin 6arayin shanu (a Arewa maso yamma), Kashe-Kashen Al'ummah Kullun abun kara girma yakeyi, 'yan ta'adda sai gawurta suke kara yi, gabadaya Arewa ta tikice; Amma babu abunda Buhari ya ta6uka. Yau an wayi gari; wa'ennan mutanen Arewa din; sun dawo daga rakiyar Buhari.
Yau sabo da tsabar Wahalar da Mutanen Arewa suke sha ta 6angarora daban-daban, har da kansu zaka ji suna cewa Buhari dai ba Adali bane, tantagareren Azzalumi ne. Wadanda suka dauki gaba damu akan Buhari; yau an wayi gari mafi yawancisu kunyarmu suke ji, basu ma so suji anyi maganar Buhari.
To wannan ya kamata ya zamowa 'yan Arewa darasi, su fahimci cewa; Ba sai lokacin da aka zalunceka ne zalunci yake zama zalunci ba, kuma duk Wanda yakeda gidan Gilas be kamata ya goyi bayan wasan jifa ba. Kada mu zamo masu goyon bayan Zalunci da Azzalumai.
Sharief Munauwar Mukhtar Gusau
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Muhimman zantuka