@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IBN QUHAFATA DA TSIKARIN UMMUL-MUMININA A'ISHA
Cikin zuciyata ina qaunar kawo falalar Sahabban Annabi (S.A.W.W )don na wannan zamani su san matsayinsu da darajarsu da kuma daukar abin koyi daga gare su.
Sai dai idan na kalli hadisan da ake kawo falalar mafi yawansu sai naji kunya, domin a fahintata qarya ce kawai da ake kawowa don rashin abin fada. Wani lokaci kuma sai naga zarafin Annabi (S.A.W.W )ake ci da sunan kawo darajar wani.
Ga dai misali cikin S ahihul-Bukhari.
Daga A'ishatu matar Manzon Allah (S)tace, mun fita tare da Manzon Allah (S.A.W.W )cikin sashen wasu tafiye-tafiye har muka iso Baida'i ko Zatil Jaish sai abin wuyana ya tsinke. Sau Manzon Allah (S )ya tsaya a tantinsa, mutane ma suka tsaya tare da shi, kuma gurin babu ruwa.
Sai mutane suka tafi zuwa ga Abubakar Siddiqu(babana )suka ce;
‘’ YANZU BA KAGA ABINDA A'ISHA TAYI BA, TA TSAYA TARE DA MANZON ALLAH ALHALI BABU RUWA (na sallah )TARE DA MUTANE ?‘’
Sai Abubakar (babana )yazo (wajen mu ) alhali kan Manzon Allah (S .A.W.W )na kan cinyata, har ma yayi bacci.
Sai (baban nawa )yace;
‘’ KIN TSARE MANZON ALLAH (S )A GURIN DA BABU RUWA KUMA BABU RUWA TARE DA MUTANA?‘’
A'isha tace, sai Abubakar ya zarge ni, kuma ya fadi abinda Allah yaso ya fada (a kaina ), SAI YA CIGABA DA TSIKALINA DA HANNUNSA A QUQUNA, BABU ABINDA YA HANANI YIN ZILLO SAI DAI KAWAI GANIN MATSAYIN MANZON ALLAH (S )DAKE(kwance )KAN CINYATA, (amma na ji tsikalin nan da yayi min )....., daga nan sai aka saukar da ayar taimama .‘’
SAHIHUL-BUKHARI, hadisi me lamba 334, 336, 3672, 3773, 4583, D.S
Abinda ake so a kawo anan shine falalar A'isha, domin a dalilinta aka saukar da ayar taimama.
TAMBAYA
-Yanzu wannan falala ce ko cin zarafin Abubakar ?
-Yanzu tsikalin da Abubakar ya riqa yiwa 'yarsa a kan cinyar Annabi da me yayi kama?
-Da gaske wannan hadisi ma ya inganta?
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN