GANI YA KORI JI:-Tabbas Akwai Gurbatattun Hadissai Da Muka Boye Bamu Sanar Daku ba !!!





DAGA CIKIN QARERAYIN ABU HURAIRA


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ANNABI IBRAHIM (A.S )YA YIWA KANSA KACIYA DA GATARI BAYAN YAYI SHEKARU 80

Za ka riqa shan mamaki yayin da ka ci karo da wasu hadisai cikin sahihul-Bukhari .

Kamar yadda Qur'ani ya kasance littafi mai dauke da tarihin abubuwa daban-dabam za muga cike yake da darusa abin koyi, domin yakan kawo tarihin mutanen kirki da ayyukansu don muyi koyi dasu. Wasu kuma na mutanen banza ne da ayyukansu da ake so mu nisance su.

Wani lokaci kuma yakan kawo mana na dabbobi ne don su zama aya gare mu don sanin girman Allah da ikon Sa, sannan cikinsa akwai umarni da hani.

To, kamar haka hadisan gaskiya na Ma'aiki (S.A.W.W )suke, sun tattaro mana dukkan siffofin abinda ke cikin Qur'ani.

Amma cikin irin hadisan qaryar da Abu Huraira ke kawowa sai kaga kwata-kwata babu darasi abin dauka daga ciki, sai ma ka rasa ma'anarsa gaba daya, amma Bukhari ya inganta shi.

Ku biyo ni don ji da gani da idanuwanku .

Bukhari yace, baban Yamani ya bamu labari, Shu'ubatu Bn Abiy Hamzata ya bamu labari , baban Zinadi ya bamu labari daga A'araj, daga Abu Hurairata yace, lalle M anzon Allah (S.A.W.W )yace;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ IBRAHIM YAYI KACIYA (wa kansa )BAYAN SHEKARA TAMANIN (80), YAYI KACIYAR NE DA GATARI (axe ).‘’

(Bukhari , hadisi me lamba 6298)

            TAMBAYA
         __________

Da ka karanta wannan hadisi dan Allah me ka gani ko ka dauka da zai zama darasi a gare ka wanda za kace ka qaru ko ka amfana daga hadisin?

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda .

ASABAR, 27th June, 2020/ 8-11-1441.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN




4 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Na koyi cewa Ibrahim (AS) mai biyayyar ubangijin shine. Domin yayi wa kanshi shayi yana Dan shekara 80 Don yin biyayyar ga umar in Allah.

    ReplyDelete
  2. Abani audio na inda kabiru gombe yayi wannan maganar ga number na 07062101293

    ReplyDelete
Previous Post Next Post