@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ALLAH YA CI DARIYA DON GANIN DABARAR DA WASU MA'AURATA SUKA YI
Sau da yawa akan qirqiri qarya don a nuna daraja ko falalar wasu mutane daga cikin Sahabban Annabi (S.A.W.W ), sai dai sai kaga babu hikima ko ma'ana cikin maganar.
Duk wani ma'abocin karatu ya san cewa aya ta 9 cikin suratul-Hashri na magana ne kan Ahlul-Bait (A.S ), amma sai aka juya ta zuwa ga wasu na dabam.
Ga dai abinda suka ce;
Bukhari ya riwaito daga Musaddadu, daga Abdullahi Bn Dawud, daga Fudhail Bn Azwan, daga baban Hazeem, daga Abu Huraira cewa;
Wani mutum ya je wajen Annabi (S.A.W.W )(a matsayin baqo ), sai ya aika zuwa ga matansa (ko za a sama masa abinci ), sai suka ce; ‘’ TARE DAMU BABU KOMAI SAI RUWA.‘’ Sai Manzon Allah (S.A.W.W )yace;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ WA ZAI GWAMA, KO WA ZAI 'DAU BAQUNCIN WANNAN ?‘’
Sai wani mutum daga mutanen Madinah yace ; ‘’ NI ZAN 'DAUKE SHI .‘’
Sai ya tafi tare shi (baqon )zuwa ga matarsa yace mata, ‘’ KI KARRAMA MIN BAQON MANZON ALLAH (S.A.W.W ).‘’ Sai tace;
‘’ BABU WANI ABU TARE DAMU IN BA ABINCIN YARA BA.‘’ Sai (mijin nata )yace;
‘’ To, ki tattara wannan abincin, ki kashe fitilarki kuma ki sa yaran naki suyi bacci .‘’
Yayin da suka so cin abincin sai ta dauke abincin nata, ta kashe fitila kuma ta sa yaran nata su kayi bacci . Sa'an nan ta tashi tana gyara fitilarta ta kashe ta, shi kuma (baqon )yana ta cin abinci bisa tsammanin su ma suna ci ne, suka wayi gari cikinsu babu komai (baqo kuma na qoshe ).
Da gari ya waye sai suka yi sammako zuwa ga Annabi (S.A.W.W , sai yace musu;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ DAREN JIYA ALLAH YA CI DARIYA KO YAYI MAMAKI BISA DABARAR DA KU KAYI (har baqo ya kasa gane cewa ku ba ku ci komai ba ).‘’
Daga nan sai Allah ya saukar da,
‘’ SUNA FIFITA WASU AKAN KANSU KO DA SUNA DA BUQATA.....‘’
(Suratul-Hashri, aya ta 9)
-Bukhari , hadisi me lamba 3798
(Wato dabarar tasu ta bawa Allah mamaki shine ya kwana yana dariya )
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH
Tare da Ado Isah Guda
09039791509
Juma'ah, 26th June, 2020/ 7-11-1441
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN