@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ANNABI MUSA YA ZARGI ANNABI ADAM (A.S )
Yana daga cikin qa'idar Ahlus-Sunnah cewa matuqar an taba samun mutum da yin qarya, to ba za a karbi wata magana (hadisi )daga gare shi ba.
Wannan tunani ya sabawa hankali da ilimi, domin akan iya samun mutum maqaryaci amma watarana zai iya fadar gaskiya , ko kuma a sami mutum mai gaskiya amma wata rana sai ya biye son zuciyarsa yayi qarya domin shi ba ma'asumi bane.
Larabawan Makkah sun shaidi Annabi (S.A.W.W ) cewa mai gaskiya ne da riqon amana, kuma kowa ya gaskata su kan haka. Amma a yayin da aka aiko shi(S.A.W.W )a matsayi Manzo sai suka ce maqaryaci ne, boka ne kuma mawaqi ne.
A fahintar Ahlus-Sunnah dole ka gaskata wadannan kafirai kan abinda suka fada , domin an san su da gaskiya, amma a wajen Allah ba haka bane.
Kowa ya san shaidan maqaryaci ne mayaudari , amma yayin da ya jagoranci kafirai a wani yaqi kuma yaga rundunar Mala'iku sai ya juya baya yace musu;
‘’ LALLE NI NAGA ABINDA BA KU GANI BA !‘’
To, a fahintar Ahlus-Sunnah sai suce wannan magana ta shaidan cewa yaga abinda ba su gani ba (Mala'iku )qarya ce .
Abu Huraira maqaryaci ne, amma qaryarsa ba za ta hana a gaskata maganarsa ba in har tayi daidai da nassin alqur'ani ko ingantattun hadisai.
Yana daga cikin qaryarsa cewa, wai Annabi (S.A.W.W )yace;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ Adam da Musa sunyi jayayya , sai Musa yace masa , ‘’ YAA ADAMU!KAINE BABANMU WANDA KA TOZARTA MU KUMA KA FITAR DAMU DAGA ALJANNAH KO ?‘’ Adam yace masa;
‘’ ALLAH YA ZABE KA DA MAGANARSA KUMA YAYI MAKA RUBUTU DA HANNUNSA, YANZU KANA ZARGINA KAN AL'AMARIN DA ALLAH YA QADDARA SHI A KAINA TUN KAFIN YA HALICCE NI DA SHEKARU 40?Sau uku Adamu na kafawa Musa hujjah!‘’
(Bukhari, hadisi me lamba 6614)
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Alamis, 25th June, 2020.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN