Sadar Yusuf Kano.
Eh hakane, ba lallai ne mu cigaba a yanda muke hakan yanzu ba.
Har yanzu da akwai fata, koda shike a haka sai mu lura kamar ba wani fata sosai.
Kada yanayin hargitsewar lamurra ya sanya mu debe kauna.
Hakanan kada sanyi da raunin akasarin 'yan uwa ya karya mana gwuiwa mu koma mu tankwashe kafafu.
Lallai akwai fatan a samu canji daga raunin mu zuwa kara motsawa haiqan.
Amma dole sai an kara samun yawa da dagewar kalilan masu yi domin Allah!
Kalilan din ba irin su gauga'u ake nufi ba, masu neman yin gangaci da haukatakun rashin nizamin da bashi da wata natija!
Ana bukatar kalilan ne masu dagewa, cikin basira da hangen nesa, da kuma uwa uba yi don Allah kadai!
Wato wadansu kalilan kenan masu zurfin tunani, gami da lissafin kyawon akibar da aikin su zai haifar!
Wadannan kalilan din lazim ne su zama masu ilimi daidai gwargwado na addini da na zamani, domin babu inda aka taba samun jahilai suka iya canja wata Al'umma ala khayrin.
Wato har wala yau, kenan ba ana neman gayyar rububi bane!
Ba kuma gayyar 'yan azarbabi ba, masu wuce gona da iri.
Ba'a da bukatuwar dole sai wasu sun rika nacewa, akan su a ko yaushe sai sunyi kokarin yin tawili da kwaskwarima a hakikanin bayanan Jagoran Harka (H).
Su wadancan kalilan din da muke zancen bukatuwarsu din, to dole ne fa suyi azamar samun tsantar ikhlasi, juriya da dakewa, da sadaukarwa, a bisa daidai gwargwadon iyawarsu.
Ma'ana ba irin wadanda zasuyi aikin da ninancin har kullum su nasu ne kawai daidai ba, har kuma su rika mummunar suka, ko aibanta sauran ma'aikata ba, suna cewa wane da wane basa wani kokari.
Ba'a bukatar masu saurin fitinuwa da kokarin bata shaksiyyar sauran Almajirai da Mabiyan Jagora (H) da sunan wai sune mafi cancantar mabiyan Jagora (H) !!!
Balle kuma masu haramben jifan duk wanda suka samu matsalar rashin fahimta, ko rashin jituwa dashi, da kalmar Dan Security!!!
Wayayyu ake nema masu faffadan tunani, ba masu wadatuwa da tsuke kwakwalen su ba.
Masu kokarin karatu da kuma kokarin aiki da karatun nasu sosai da sosai, ba masu yawan aiki da adifa da soye soyen zukatan su ba.
*Allah T Shi ganar damu, tunda yardar Allah muka zo nema ba yardar da zukatan junaba!!!*
Allah T Shi gaggauta bayyanar mana da cikakkiyar hurriyyar jagora (H) da sauran 'Yan'uwa duka.
*Ya kuma kawo mana karshe tare da ikon cinye wannan babbar jarabawa*
_Ilahee Ya Rabb._
Bissalam.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Jagoran Gaskiya