:
---------------///------------
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad.
To ance zan bada labarin yadda waqian Maulud {12 Dec, 2015} ta rutsa damu. To insha Allah zan fara yanzu:
-A wannan rana muna filin makarantar fudiyya don koyawa yara parade sai kwatsam muka hau whatsapp sai mukaga sojoji a husainiyya harma sunyi harbi.
-Ana haka sai wani dan uwa ya kiramu yana gaya mana cewa "wadannan sojoji Malam zakzaky suke son kashewa, ana bukata yan uwa su iso Zaria gidan malam tun da wuri.
A nan NE muka Hadu mu 4 da shahid zaharaddin musa, shahid Nazir tijjani da ni me magana da wani abokinmu mai suna mujittaba
Muka fara fafutukan neman kudin mota, bamu iya samu ba har sai da yamma tayi.
Kowa yayi sallama da gida muka kama hanya. Muna tafiya cikin raha da abokan mu, Ashe Tadin karshe mukeyi mu bamu sani ba,
A wannan ranar mun Dada shakuwa da shahid zaharaddin da shahid nazir Ashe na karshe ne,
Muna cikin tafiya har dare yayi mun zo kusa da wani gari da ake cewa magama gumau, kwatsam sai mukA ga go slow.
Isarmu ke da wuya sai mukaga Ashe sojoji ne a gaban mu sama da Bus 12 sunyi convoy Sun nufi Zaria.
Sai muka kira shahid ukasha idris muka bashi report. Daga nan muka wuce su muka nufi zaria muna hiran mu a mota, shaheed Naziru yanata kiran family su yana musu ban kwana kai kace yasan zai yi Shahada
Haka dai muka isa Zaria dare yayi. Mun iske Zaria tayi shiru komai ya tsaya cak
Mukayi waya akace mu tsaya a darurrahma.
Muyi ta addu a in safiya tayi sai mu karaso gidan sayeed Zakzaky h.
Haka kuwa muka kwana.
Mun sami masu duty muka gaisa da muka gama addu oi muka fito muna taya su duty.
Daga nan muna jin irin ruwan wutan da ake yi a gyallesu ana kiranmu a waya ana gaya mana irin kisan da sojojin Nigeria Sukey akan yan uwanmu.
-Shaheed zaharaddin ya shiga daki ya shafa mai yana cewa kar azo masa wanka in yayi Shahada a ganshi da fararen kafafu
Da ya gama sai muka ce mu kwanta ko baccin awa 1 ayi saboda mu tashi da karfin mu gobe mu tunkari azzalumai.
Mun kwanta amma sam bacci baizo ba har zuwa Asuba.
-Sai muka fito sallah anan ne muka ga Sauran yan Bauchi muka gaisa dasu shahid ukasha aka tafa aka karfafa juna sai muka wuce cikin masallaci don sallan asuba
Mukayi sallah a bayan shahid uksha muka idar.
Sai muka fita don debo jakanmu.
Da muka debo sai muka kaman hanyan fita daga darurrahma don muje gidan malam.
Isarmu gate keda wuya sai kawai muka ji anacewa ga sojoji muna daga kai sai muka hangesu with full arms suna kokari zagaye mu amma unfortunately mu mun fita bakin gate sai basuji dadin fitowanmu ba,
Anan babbansu yazo yana magana damu cewa mu koma ciki muka ki har ya zama an fara sa insa da wasu sisters
Da sukaga munki Bin umurnin nasu kawai sai yabada order na harbi anan suka bude wuta ba kakkautawa mukace sisters Sun kwanta sai suka kwanta.
Sai ya zama harbi yayi bibbiyu ciki ana harbin yan uwanmu da suke masallaci wasuma suna sallah waje kuma ana harbinmu mu da mukayi niyan zuwa gyallesu.
-Harbi ya tsananta mu kuma kabbara mukeyi domin babu mai ko sanda cikinmu.
Sun Razana mu haka Sun farraka mu. Da mukaga mun dawo yan kadan sai mukace sisters suje mun dauke musu
Sai yazama bamufi mu hudu ba a waje muna jefa dutse can saiga Muhammad Sani ya fito daga ciki an ji masa ciwo a fiska sai mukayi Sauri mukaje yanda yake sai yace mana ai an harbe su malam uksha, muna kwance sai mukaga malam sa 'ad mai kiwon dabbobin nan ya cire adda yabi sojiji da gudu
Suna gudu sai muma muka bisu suna harbi amma sabida gudun dasukeyi bindigan na jan su.
-Haka muka rakasu har kusa da kabarin su sayeed Ahmad malam sa ad na gaban mu. Bamu ankaraba sai mukaga wasu sunyi squatting kawai sai suka bude mana wuta anan malam sa 'ad yayi Shahada.
Ni da Muhammad sani da Ammar mafatihu muka juya da gudu muka nemi cover,
Can sai mukaji harbi ya tsaya sai muka shiga ciki muna lekawa sai mukaga ba sojojin sai muka shiga masallaci da gudu.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,
Jini ne ke gudana a masallacin kaurin wuta kake ji tsabar harbi, wasu kasusuwansu kake gani a waje,Wani kwakwalwar sa ne a waje,
Wani kafarsa ya balle,
Wasu suna kokarin cikawa suna kalmar shahada,
Wasu kuwa Sun riga Sun cika,
Bamu taba ganin tashin hankali kaman na ranar ba
A nan nake tambayan sani meye abinyi sai yace min first aid, sai nace arresting bleeding to sai muka fara daure gurin harbin wasu.
Wasu kuma ana kokarin fitardasu
Wasu kuma dama ba a harbesu ba duk akayi waje dasu.
Aka barmu daga mu sai wadanda suka ji mummunan rauni.
Naje na rike shahid naziru abokin tafiyana ina rarrashinsa yana cewa na bashi ruwa cinyarsa ya karye
Yana cewa na bashi ruwa ina bashi hakuri.
Shi kuma Muhammad Sani yaje nemo mana abinda zamu shimfida naziru a kai mu daukeshi
Muka dauki shahid naziru mu uku akan katako gashi yayi tsananin nauyi gashi duk ji
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Muhimman zantuka