Masu zanga-zanga a garin 'Yan Tumaki da ke karamar hukumar Dan Musa da ke jihar Katsina sun bankawa hoton Shugaba Buhari wuta.
Rahotonni na nuna cewa masu zanga-zangar suna yi ne don Allah wadai da kashe-kashen da 'Yan bindiga ke musu, wanda gwamnatin Buhari ta kasa tsinana komai wajen dakilewa.
Mazauna yankin sun ce tsawon kwanaki Mahara kan je kauyukansu su ci karensu ba babbaka, ta hanyar kashe wanda suka so, da sace wanda suka so, kuma suna iya shafe awanni suna yi, ba tare da ko jami'i guda na gwamnati ya zo ba. Kuma haka bai hana gobe su dawo su kara irin na jiya din, ba wani matakin da ake dauka.
Maharan kan shiga gidajen mutane su ci zarafin matansu, su ketawa yaransu mutunci, kuma su fito kansu tsaye su koma mafakarsu lami-lafiya. A yayin da suke buge duk wanda suka ga dama, ko su raunata.
Idan har da gaske ne gwamnati na son kare lafiyar al'umma, to ta mai da hankali ne kan wadannan maharar, ta kyale mutane da batun Corona haka. Domin a rana guda Maharan nan kan kashe mutanen da a tsawon wata biyu Corona bata kashe su ba.
MDN BARA`A MALUMFASHI
M.N.N. U
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Labaran Duniya