Akwai Abin Mamaki Cikin Al'amarin Mumini!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DUK WANI AL'AMARI NASA ALKHAIRI NE

Idan muka bibiyi tarihin Annabawa da Manzanni (A.S )za muga al'amarinsu abin sha'awa ne ga dukkan mumini, kuma suka zama abin koyi ga wanda yayi imani ga Allah .

Cikin wannan al'umma da muke raye cikinta akwai bayin Allah muminai wadanda ayyukansu da zantukansu ya siffantu dana Manzanni (A.S ).

Kuma al'amarinsu kan qara bayyana ne qarara yayin da irin cutarwat da aka yiwa Annabawa (A.S )ta shafe su. Babu firgici, ba gigita, ba kasala, sannan babu nadama tare dasu.

Za su baka mamaki cikin tawakkalinsu ga Allah wajen yarda da dukkan hukuncin da yayi a kansu, wato ba sa canzawa daga abinda suke yi zuwa bin son zuciyar wani ko wasu, ko da kuwa za su rasa ransu ne.

Wannan dalili yasa Manzon Allah (S.A.W.W )ke yin mamaki game da al'amarinsu kamar yadda yazo cikin wani hadisi daga Sa'ad Bn Abiy Waqqas cewa Manzon Allah (S.A.W .W )yace;

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

‘’ INA YIN MAMAKI GAME DA HUKUNCIN ALLAH (T )AKAN MUMINI, IDAN WANI ALKHAIRI YA SAME SHI SAI YA GODEWA UBANGIJINSA (a zuci ), YA KUMA GODE MASA (a bayyane )(Hamdan wa shukran ). IDAN KUMA WATA MASIFA CE TA SAME SHI SAI YA GODEWA UBANGIJINSA KUMA YAYI HAQURI (kan wannan jarrabawa ). ALLAH NA BADA LADA GA MUMINI CIKIN KOMAI, HAR CIKIN LOMAR DA YAKE DAGATA ZUWA BAKIN MATARSA .‘’

(Musnad Ahmad, J:1, SH:173 ).

Yanzu duk wanda yasan irin zaluncin da aka yiwa Sayyid Zakzaky (H )zuwa yanzu, kuma ya ganshi a zahiri da jin kalamansa zai san cewa lalle shi mumini ne na kwatance.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

         09039791509

Juma'ah, 19th June, 2020/ 29-10-1441

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post