@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
UMAR BN KHADDABI YA QALUBALANCE SHI
Babu wani abinda Allah ya rage cikin alqur'ani wanda bai yi bayaninsa ba, sannan Annabi (S.A.W.W )ya fayyace mana komai daki-daki don kada mu fada cikib rudani ko hadari.
Cikin hadisinsa (S.A.W.W )yake cewa, ‘’ Duk wanda yace la'ilaha illal-Lahu jininsa da dukiyarsa ta haramta a gare mu, sai dai bisa haqqinsa (wato ya warware wannan kalma ).‘’
Bayar da zakkah na daga cikin rukunan muslimci , amma ba ya daga cikin abinda ya zama wajibi ga kowanne musulmi , domin ba kowa ne ke da halin bayarwa ba, ita kuma tana wajaba ne kan mai iko.
Na'am, qin bayar da iya ga wanda ke da iko kan iya dawwamar da shi cikin wuta, amma ba ace ka kashe shi don ya qi bayarwa ba, domin wani haqqi ne tsakaninsa da Ubangijinsa.
Bisa sahihiyar magana babu wanda ya qi bayar da zakkah daga cikin sahabbai bayan wafatin Annabi (S.A.W.W ), sai dai an sami wadanda suka ce su ba za su bayar da ita ga wanda Allah da Manzonsa (S )bai yi wasicci da shi ba (wato Abubakar ).
Kan hakane Abubakar ya halasta jinanan muminai da sunan wai sun qi bayar da zakkah sun raba tsakaninta da sallah .
Bukhari ya fitar cikin sahihinsa daga Abu Huraira yake cewa, yayin da Annabi (S.A.W.W )yayi wafati Abubakar ya zama khalifa , wadanda suka kafirta suka kafirta daga larabawa sai Umar yace,
‘’ Yaa Abubakar!Ta yaya za ka yaqi mutane alhali Manzon Allah (S.A.W.W )yace;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
‘’ AN UMARCE NI DANA YAQI MUTANE HAR SAI SUN CE LA'ILAHA ILLAL-LAH, DUK WANDA YACE, ‘’ LA'ILAHA ILLAL-LAHU HAQIQA DUKIYARSA DA RANSA SUN TSIRA DAGA GARE NI SAI DAI BISA HAQQINSA, KUMA HISABINSA NA WAJEN ALLAH (ba a hannunmu ba )?.‘’
(Bukhari , hadisi me lamba 6924)
Wannan aikin da Abubakar yayi shine na yanzu suka dogara da shi wajen halasta jinanan muminai.
ALLAH KA RABA MU DA BATA BAYAN SHIRIYA .
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Laraba, 24 2020
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN