Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya bayyana dalilinsa na rashin zuwa jana'izar ko jaje zuwa garuruwan da 'yan bindiga suka kashe mutane a jihar Katsina.
Duk da cewar da wuya ayi min wani abu, amma wallahi ina tsoran zuwa wani wurin. Saboda da kaina na je na ce masu zaa samu zaman lafiya a mafi yawancin wadannan garuruwan da 'yan bindigar ke kai hare-hare, an zo ba a samu zaman lafiyar nan ba, ka je ka ba su hakuri na ukku mi za ka ce masu, da ka yi magana za su ce karya ka ke, ba ni da hujjar da zan kare kaina
Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai dangane da halin da jihar Katsina ta samu kanta, na matsalar tsaro, wanda ya gudana a gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Masari ya kara da cewa "Muna son mu je mu jajantawa al'ummar nan, mu gwada masu mun damu. To amma da wane ido za su kalle ni, shi ke hanani zuwa. Inda ace ko wata girgizar kasa ce ko ambaliyar ruwa, da tare da ni za a yi masu zana'idar. Amma yanzu da sun ganni cewa za su mi na zo yi?
Gwamna Masari ya cigaba da cewa "hare-hare da 'yan bindigar ke kaiwa a kwanan nan, yafi annobar cutar Corona tashin hankali. Covid 19 kwata kwata a jihar Katsina mutum ashirin da daya, wanda muka sani. Shi kuwa hare haren yan bindigar a cikin satin nan kawai sun kashe sama da mutum hamsin. Haka kuma bai wuce wata guda ba, 'yan bindigar nan sun hallaka mutum arba'in da daya tsakanin Dutsinma da Safana da kuma Danmusa. Ban da wadanda ake kashewa daya biyu kusan yau zama ruwan dare a jihar Katsina. Ga asarar rayuka ga zaman dar dar, ga shi kuma sun talauta su.
Daga karshe Masari ya ce Gwamnatinsa za ta ci gaba da taimakawa jami'an tsaro, dai dai aljihun gwamnati, mun yi kuma za mu cigaba da yi. Har abinda bai kamata ba mun yi saboda mun shiga cikin daji domin yin sulhu da su, kuma mun cika masu Alkawarin su, Amma su sun karya. Za mu cigaba jami'an tsaro dukkan goyan bayan da ya dace domin kawo karshen wannan kashe kashe.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Labaran Duniya