Yanzu Ƙarfin Mu, Duk Yana Ƙare Wa Ne, A Faɗa Da Junan Mu – Sayyid Zakzaky

Jarida Domin Kai da Al'ummar ka!

Daga Bin Haroun Sigau

Akwai wani lokaci da wani ‘channel’ har ma na daina sauraronsa, ‘channel’ din na satalayit ne. Wani ‘channel’ ne na Larabci amma na kirista. To sai na ga wani haka kamar Balarabe suna sa wani abu kamar
rawani baqi da kuros dinsa, yana da littattafan addini daban-daban na
Musulunci, da ma ‘research’ da wadansu musulmi suka rubuta ‘against’ wasu musulmi.

Akwai wani ya rubuta ‘research’ wai shi ‘Usulus Shi’a’. Ya yi ta jafa’i irin wanda ya so aka ba shi digirin ‘Phd’. To sai na ga ya dauko wannan. Kuma yana duba Mauqib dinsu a intanet. Ya ce duba www.kaza inda wannan musulmin yake antaya wa wadancan Musulmin abu kaza. Sai yana ta nunawa. Ya ce, to wannan ya nuna duk addinin nasu haka ne. Wannan ya ce wane kaza ne, ka ga shi kaza ne. Wannan kuma ya ce kai ma kaza ne, ka ga duk cikansu kazan ne.

LATSA NAN👇
☞ ͡Wafatin Nana Khadijah (S.A), Goma (10) ga watan Ramadan
☞ ͡Bazan lamun ta ba, Har sai naga Almajiri na ƙarshe ya bar Jahar Plateau – Lalong
☞ ͡Alaƙar Gwamna El-Rufa'i Da Shaiɗan
☞ ͡Disease Associated with our Sanitary Condition

Har ma na tsaya ina kallo. Wata rana da na ga abubuwan dai sun yi yawa, kullum nakan ga ana hira da shi, sai na ga shi kenan dai ba na buqatar in rinqa kallo, sai na kulle tashar na daina kallo. Amma abin da na fahimta ya riga ya wadatar da ni, raunin musulmi ya ba maqiya dama. Yanzu qarfinmu duk yana qarewa a fada da junanmu. Lallai kam za ka ga wasu har da huci suna haki, suna fada da yan uwansu kenan. Amma da zarar da maqiyinsu ne, lakwas! Sai ka ga ba qarfin a nan, sai kowa ya yi basha da baki. Ya ce ai ‘Allalurat tubihul
mahazurat!’ Wadannan mutane, an ce abin da ba ka za ka iya ba, ai shi
kenan, haka nan. Amma in da dan uwansa ne yana da qarfi!

Sheikh Zakzaky A wani ɓangare na littafin 'Koyi Da Rayuwar Manzon Allah (S)' wanda Musa Muhammad Auwal, ya rubuta.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post