Rbtw: Sayyada Ummu Subaykha
Sayyada Subaykha macece Mai daraja. da girman matsayi, lokacin da zata haifi imam jawad (AS) anga karamomi masu yawa atare da ita, ibn shahar A,asub ya ruwato hadisi daga Hakima yar imam musa Alkazim (AS) ta ce, ;lokacin da khaizaran ta zo haihuwa imam Riddah,yacemin "Hakima ,ki halarci wurin haihuwarta ,ki wakilceni awajanta ,ki zamo mai karbar gida."sai yasanya Mana fitila a dakin ,ya rufe mana qofa ,lokacin da naquda ta kama ta,saรฏ fitalar ta mutu a gabanta ,sai ga hasken Abun ja,afar ya haskaka wurin,(ma,ana, an haife shi kenan)tare dashi akwai wani abu marar kauri kamar tufafi(a lullube dashi ) haskensa yana qaruwa har dakin da muke ya haskake ,ya zamo muna ganin komai .sai na karbe shi na dorashi aka cinyoyina sai na cire masa wannan yanar da ke lullube dashi,sai imam Ridah (as) yazo yabude kofa yashigo a lokacin mun kammala kimtsa shi sai ya karbeshi ya sanya shi a wani kyalle Mai kyau ,sai yacemin ya Hakeemah ,ki daura masa wannan qyallen "
DANNA NAN DON KARANTA WรSU MUHIMMAN BAYANAI๐
☞ ͡Abinda baka ji ba, ba kuma zaka taษa ji ba daga bakin Buhari
☞ ͡Zaman zikira domin tunawa da waki'ar ษan uwa Musa Hasan Shinkafi da Sojoji
☞ ͡Hikima Kayan mumini Part 8
☞ ͡Subaykha Annubiyya Mahaifiyar Imam Jawad (AS)
Sayyida Hakeemah taci gaba da cewa "a rana ta uku,(jaririn) ya daga idonsa zuwa sama , sannan ya kalli damansa da hagunsa,sai yace "na shaida bawani Ubangiji sai Allah na shaida cewa Muhammad manzon Allah ne "sai na miqe tsaye cikin firgita da tsoro! Sai nazo ga baban Hasan (as) na ce Masa naji abin mamaki agun wannan yaron (JAWWAD) sai yace me yafaru ? Sai na bashi labari cewa (naji yaron yace Ashhadu Alla ilaha illallah,wa Ashhadu Anna Muhammadu rasullah !) Sai yace Hakeemah! Abinda nagani na abubuwan mamaki a wurinsa yafi naki yawa daban Al,ajabi)"
(Manaqib,juzu,I na 4 shafi na 395).
Haihuwar ya'ya masu cikar Kamala da daraja ba kawai bisa hadari yake samuwa ba, dole akwai wani tasiri na kyan hali da dabi,un Kamala daga iyaye ,musamman mata. Duk mai fatan samun da ko ya'ya nagari to dole tayi qoqari na siffantuwa da siffofi da halaye irin na Sayyida Subaykha Annubiyya (as)
Ya Allah kabamu ikon koyi da salihan bayinka ka azurtamu da ya'ya nagari masu albarka. Anan nakawo karshen wannan tarihi na wannan baiwar Allah dftn zamuyi amfani da darasin da ke ciki da kuma gyara agaremu inda mukayi kuskuri๐๐ป.
Sayyada Ummu Subaykha lafia
#GovernmentFreeZakzaky
Wasu Labarai Anan>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Tunatarwa