@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SHARI'A MATAKI NE NA BARRANTAR DA SHI
Allah shine masanin zahiri da badini, kuma shine mai warware dukkan wani makircin makirai.
Cikin iliminsa (S.W.A)da kuma wata manufarsa wacce yake son bayyanar da ita ga azzalumai, masu goya musu baya da ma 'yan ko-in-kula game da wannan zalunci da aka yiwa Sayyid (H)da mabiyansa yasa dukkan wannan matakai da ake ta bi na shari'a (shiga kuto)ke aukuwa.
Waqi'ar da aka yi ta Zaria 2015 wacce jami'an tsaron Nigeria suka jagoranci afkar da ita bisa umarnin Buhari (The chief security of the army forces)don farrantawa Yahudawa da kuma yunqurin ganin bayan tasowar ruhin muslimci, ya sa suka qirqiri qarya wacce suka fake da ita a matsayin hujja na dirarwa raunana marar sa makamai a hannunsu a garin Zaria.
DANNA NAN DON KARANTA WÀSU MUHIMMAN BAYANAI👇
☞ ͡Abinda baka ji ba, ba kuma zaka taɓa ji ba daga bakin Buhari
☞ ͡Zaman zikira domin tunawa da waki'ar ɗan uwa Musa Hasan Shinkafi da Sojoji
☞ ͡Hikima Kayan mumini Part 8
☞ ͡Subaykha Annubiyya Mahaifiyar Imam Jawad (AS)
Tun wancan lokaci ake ta faman yin shari'o'i a kotuna daban-dabam, wasu 'yan'uwa ne ke shigarwa, wasu kuma azzaluman ne ke shigarwa, amma a qarshen kowacce shari'a raunana ne 'yan (Shi'ah)ke yin nasara.
Zuwa wannan lokaci wasu sun fahinci cewa lalle an zalunci Sayyid Zakzaky (H), wasu kuma da sauransu tukunna.
Wannan shari'a da fitowarsa(H)za tazo qarshe ne yayi da Allah ya gama wanke shi daga sharrukan da akayi ko ake masa.
Wannan dalili ne ma yasa Sayyid (H) bai taba hana lauyoyinsa shigar da qara wajen nema masa haqqinsa ba.
‘’ HAKAN KUWA (na faruwa ne)DON YASAN CEWA LALLE NI FA BAN HA'INCI SHI A BOYE BA (wato babu wanda a ha'inta a qasa), KUMA LALLE ALLAH BA YA SHIRYAR DA MAKIRCIN MAHA'INTA (maciya amanar talakawansu).‘’
(Suratul Yusuf, aya ta 52)
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~1st May, 2020.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Jagoran Gaskiya