Salloli Biyar Masu Lokuta Uku..





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

HADA SALLOLI SUNNAR ANNABI (S.A.W.W)CE

Munyi wannan gajeren rubutu don yaye wata subha wacce wasu bangaren musulmi ke aibanta bangare dangane da hada salloli ba bisa wata lalura ba.

Ita dai sallah wacce Allah (T)ya wajabtawa bayinsa yinsu a kullum guda biyar ne masu lokuta uku. Qur'ani ya ambaci hakan, sannan kuma hadisi ma ya kawo.

Ma'ana salloli na kullum (yaumiyyah)lokuta uku ne dasu ba biyar ba, wanda hakan ke nuna mana ana iya yinsu a lokuta uku ba dare da zargin juna ba.

Allah (T)na cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ KA TSAYAR DA SALLAH A KARKATAR RANA ZUWA GA DUHUN DARE, DA KUMA LOKACIN FITOWAR ALFIJR, LALLE KARATUN ALFIJR YA KASANCE WANDA AKE HALARTA .‘’

(SURATUL-ISRA'I, AYA TA 78)

Lokuta uku da aka ambata anan sune:-

-Karkatar rana (Azahar da La'asar).

-Duhun dare(Magrib da Isha'i).

-Fitar Alfijr (Asuba).

LATSA NAN👇
☞ ͡Wafatin Nana Khadijah (S.A), Goma (10) ga watan Ramadan
☞ ͡Bazan lamun ta ba, Har sai naga Almajiri na ƙarshe ya bar Jahar Plateau – Lalong
☞ ͡Alaƙar Gwamna El-Rufa'i Da Shaiɗan
☞ ͡Disease Associated with our Sanitary Condition

Bukhari ya riwaito cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

Baban Nu'uman ya bamu labari yace, Hammad ya bamu labari, shine Ibn Zaid, daga Amru Bn Dinar, daga Jabir Bn Zaid, daga Ibn Abbas cewa, ‘’ ANNABI YAYI SALLAH A MADINAH RAKA'A BAKWAI DA TAKWAS, AZAHAR DA LA'ASAR, MAGRIBA DA ISHA'I .‘’ Sai Ayuba yace; wataqila lokacin ruwa ne, sai Jabir Bn Zaid yace, wataqila .‘’

(Bukhari, hadisi mai lamba 543).

A wani hadisi kuma kuma, ....na ji baban Sha'athaa'i Jabir yace;da na ji Ibn Abbas (R.A)na cewa; ‘’ MUNYI SALLAH TARE DA MANZON ALLAH (S.A.W.W)(raka'o'i)TAKWAS A HADE DA KUMA BAKWAI A HADE.‘’ Nace, ya baban Sha'athaa'i, ni dai ina zatonsa ya jinkirta Azahar ne ya gaggauta La'asar, kuma ya ya gaggauta Isha'i ya jinkirta Magrib. Yace, ni ma dai haka nake zato .‘’

(Bukhari, hadisi me lamba 1174)

Idan muka kalli wadannan hadisai za muga sun fassara mana ayar saman ne fassara ta haqiqa.

Na'am, ba wai so nake na kore hadasu ba, amma dai so nake ka fahinci cewa ana hadasu ba wai sai da wata lalura ba, domin lokacin nasu daya ce.

Domin da aka tambayi Ibn Abbas ma don asan wacce lalura ce ta jawo hakan, sai yace; ‘’ YAYI HAKAN NE KAWAI DON KADA YA QUNTATAWA MUTANE .‘’

Dan Allah a nisanci kame-kame wajen magana.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

         09039791509

~4th May, 2020.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post