Iyali A Muslunci Fita Na Huɗu (4).. Halayya Na Gari, Tare Da Riƙo Da Addini

Shafi Domin Kai Da Al'ummar Ka



Daga Bin Haroun Sigau

Yazo a ruwayoyi da isnadi daga Manzon Allah (S) yace; "Idan wani yazo muku, kuka gamsu da addinin sa da kuma kyawawan ɗabiun sa, to, ku aure shi" kun ga kenen wannan magana ta Manzon Allah ta gama warware komi, Akwai kuma ruwayoyi da suka kawo cewa; In zaku yi aure, ku auri mace don kyawun ta, dukiyar ta, nasabar ta, da addinin ta, harma a ƙarshe yace; amma ku auri mai riƙo da addini shi yafi."

Haƙiƙa a wannan zamani mutunin kirki, mutumin banza ko mutumniyar banza, burin kowa shine samun abokin zama na gari wanda shine farkon abinda mutum ya kamata ya fara duba wa. In kace, zaka auri mutum don kyau ne, to ka tuna akwai tsufa, in don dukiya ne, to ka sani Allah zai iya karɓar abin Sa duk sanda yaso. In kuma don nasaba ne, nan ma Allah yakan jarrabci al'umma, sai kaga iyayen mutum da ilahirin dangin sa/ta mutanen kirki ne shi/ itan sai kaga akasin haka sam bama suyi kama da ahlin su ba a tarbiyya.

To, anan muna iya cewa, ka auri mutum don r̃iko da addinin sa shi yafi, domin ma'abocin addini shine mutum mai godiya a yayin samu da rashi. Harma yana daga sharadin imani, yarda da kaɗɗara, amma in mukai duba kuma da lokacin nan, sai zama ansha banban ba'a bawa mutum aure sai ɗan manya ne shi (ɗan masu kudi) ko shi kan shi mai ƙudi ne, ko kuma kaji namiji yana cewa shi auren jali zaiyi, sai ƴar mai kudi zai aura. Ya manta arziki da rashi duk na Allah ne.

Al'muhim dai shine, namiji ya zama mai ƙokarin neman na kan sa. Kuma dama yana daga irin binciken da iyaye kan yi kafin su aminta maka zuwa wajen ɗiyar su, a tabbatar zaka iya riƙe ta, d ɗan abin da kake samu da gumin ka. Sai kuma lafiyar ma'aura ta, harma a wajen yin abin da muke kira da Siiga, sai an tambayi lafiyar yaro dana yarinya. Yanzu zamanin da muke ciki zaka ga abubuwa kala-kala, waɗan da ada babu su kamar kwaji da ake zuwa kafin aure. Lallai, wannan yana da gayar muhimman ci, harma kasashen da suka ci gaba zaka ga ba gwajin cuta mai karya garkuwar jiki kaɗai ba, har da irin cututtukan nan da ta dalilin su ne ake haifo yaro da cutar Faralayis, zaka ga suna gwada wa kamin aure. Wasu ma har akan iya haƙura da juna in aka fahimci zai zama da matsala wajen haifo yara a tsakani.

To, anan zamu iya cewa yana da kyau a kula kuma ya zam masoyan da zasu yi aure susan cewa; auren nan da zasu yi bin umurni ne, wanda ta kiyaye aikata aikata haƙƙoƙin shi zasu kai ga samun tsira daga azabar wuta. Kar mu ɗauki aure kamar yadda sauran aama ɗin mutane ke ɗauka, sai kaji namiji yana cewa, ni yadda na ɗauki mace kamar cire takalmi ne, haka nake kallon su, wa iyazu billah...

Wajibin ma'aura ta ne, su haɗa kan su, su kuma fara tsara yadda zasu yi rayuwar su mai kyau a gidan ibadar su, tun kafin a ɗaura musu aure anfanin samartaka kenen in bamu sani ba, domin in abin sai anyi aure ne za'a yi tsarin zama da kuma aikata shi, abubuwan zasu dagule, za'a ji da aikace-aikacen gida ne koda tsaya wa tsara rayuwa. Da Kuma neman sanin abubuwan da juna ke so da wanda bai so, zaifi bada natija ku san dukkan abinda ɗayan ku yake so, abinda ke saka shi farin ciki, da yanayin da ana ganin ɗayan ku, zaku gane wannan fa! Akwai matsala, sai a nemi hanyar gyara wa, da raba shu da matsalar dake damun sa.

Abu na ƙarshe kuma shine, miji da mata ana son su kasance masu rike sirri, aure abu ne mai buƙatar sirri ba'a ɗaukar matsalar gida ake yawo dashi cikin majilisu, ƙawaye da sauran su, ku zama kamar duniyar ku, ku kaɗai ke cikin ta, in matsala ta faru tsakani, ku cinye ta a ɗakin ku ba tare da wani yaji ba, ku sasan ta kanku. To, in kukai haka, zai zama ginin iyalin ku, kullum ƙarfi zai kara yi kamar ginin da akai da tubalin ƙarfe..

Allah ya iya mana badon halin mu ba, ya zaɓa mana mata/maza na gari. Ya kuma azurta mu da haifar tsarkakakkun bayi wanda zasu ci gabantar da wannan kira Na Manzon Allah (S).

Zamu ci gaba......

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post