Nasir Isah Ali
Maimakon gangami da zanga zangar da aka saba yi duk shekara kan masallacin Qudus,bana za'a maye gurbin gangamin ne da wasu tarukan karawa juna sani da kuma wasu shirye shiryen masu kayatarwa a madadin gangamin na Qudus. An samu wannan canjin ne sakamakon bullar cutar Corona baros mai kisa far daya,wanda kuma an fi dauka ne sakamakon cudanyar jama'a.
-
Da yake magana da manema labarai a yau lahadi a birnin Tehran,shugaban shashin dake kula da Da'awa da kuma tsara hanyoyin Isar da sakon musulunci, Birgediya Janaral Ramereza Shareef ya bayyana cewar,bana babu gangami ko zangazangar ranar Qudus sakamakon babu yanayi mai kyau na yin hakan, maimakon hakan,an tsara wasu bukukuwan da tarukan na daban wadanda zasu maye gurbin gangamin.
Wannan ya biyo bayan rufe duk wasu wuraren tarukan jama'a ne da kuma wuraren yin gangami da ibada a fadin kasar ta Iran ne.
-
Birgediya Sharif ya kuma bayyana cewar,jagoran addini Ayatullahi Ali Khamnei (DZS) zai gabatar da jawabi ga duniya a ranar ta Qudus (May 22)
Kuma zamu yi amfani da damar wajen karbar sakonnin batanci da kushe akan Israila daga ko'ina cikin fadin duniya.
Birgediya Ramereza Sharif ya bayyana cewar,babban bako a wajen wannan bukin na Qudus shine jagoran sashin siyasa na kungiyar HAMAS wato Ismail Abu Haneye. Wanda zai bayyana da kansa a birnin Tehran,idan hali yayi. In kuma wakilci aka samu duk dai masha Allah in ji Janar Shareef.
-
Ita dai ranar Qudus ta duniya marigayi mu'assisin jumhuriyar musulunci ta Iran,marigayi imam Khumaini (QSS) ne ya assa ta a 1979 bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran. Inda yayi fatawar cewar duk juma'ar karshen ko wanne watan azumin Ramalana ya zamo rana ce da musulmin duniya zasu fito domin nuna goyon baya da tausayawarsu ga mutanen Falastinu,wadanda bisa taimakon Ingila aka kwace kasar Falastinu aka bai wa Yahudawan yan kama wuri zauna.
Tags:
Labaran Duniya