In Na Bar El-Zakzaky Wa Zan Kama?? – Abba Gano





Tabbas zuciyata ta nutsu dakai Sayyid Ibrahim zakzaky, domin na duba nakuma bincika amman nagaza samun irin ka.

Lokacin danai duba wajan ibadun ka , sai natuno wata maganar ka tun 2009 dakake cewa, kayi shekara 40 kana bautar Allah da yaƙini.
( وَالَّذِينَ يَبِيتُونَ لِرَبِّهِمْ سُجَّدًا وَقِيَامًا )

Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayuwa a wurin Ubangijinsu.

Lokacin dana bincika don nemo cikakken mumini wanda yake bin Allah a dukkan Umar nin sa, nanma sai nakasa ganin wanda yake saman ka.
( قَدْ أَفْلَحَ الْمُؤْمِنُونَ )
Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ.

Dana dawo fagen haƙuri da yarda da ƙaddara nan ma saina rasa wanda iya haɗaka dashi a fagen haƙuri, don kaine aka kashewa ƴaƴa 6 amman bakayi ko raki ba.
(وَاللَّهُ يُحِبُّ الصَّابِرِينَ )

Kuma Allah yana son mãsu haƙuri.

Danai bincike don gano wanda yafika ilimi da aiki dashi, nan ma duk wanda naɗauko komi ilimin sa sai naga yagaza ka.

يَرْفَعِ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ

Allah nã ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajõji mãsu yawa.

Dana zo binciken kyauta na Sayyid zakzaky saina tuna sanda aka bashi mota, kyauta, amman ko gida bai shiga da ita ba, shima yabada ita. Sannan natuna irin kyautar dayake bawa ɗalibai in zasu makaranta. Gaskiya a fagen kyauta ma narasa mai irin nashi.

( الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ)

Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.

Tayaya zanbar mai irin wannan halayen natafi neman wanda yagaza shi?

Mutuƙar zaka rabu da abu to kasamu wanda yafi wannan abin, to Ni kuma narasa kamar zakzaky gaskiya.

Duk malamin dana ɗauko nagwama shi da Sayyid zakzaky saina ga yakasa taro shi.

Allah ka tabbatar da digaganmu a ƙarƙashin biyaiyar SHEAK IBRAHIM AL-ZAKZAKY

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post