Yawan shekaru ba shine gima ba a harka, sallamawa ce!!





@ MA'ASUMAH MIGERIAN NEWS UPDATED @

GARGADINKA NAKE DON KADA TUNANINKA YA ZAMA IRIN NA SU IBN KHADDAB

Wannan abu ya zama wata matsala ga wasu ma'abota harkar gwagwarmaya da suke gani ko tunanin yawan shekaru a harka wani abu ne da zai iya maida su manya cikin harka.

Ta wata fuskar hakane, domin samun manya cikin kowacce tafiya na qarfafarta tare da samun wata kariya sakamakon ganinsu a ciki. Duba tarihin muslimci ka gani!

Amma a wata fuskar dole sai sun kasance masu sallamawa da kuma fikira ta iya isar da saqon Allah kafin su zama manya a tafiya.

Ilimi da sallamawa na mayar da yaro ya zama babba, kuma dole masu yawan shekaru su sallama masa matuqar don Allah suke yin abinda suke yi.

Babu laifi don an dora wasu manya cikin gudanar da wasu al'amra, domin wani lokaci a kanga yawan shekarunsu sai a sallama, kenan su ma akwai nasu matsayi na musamman. Annabi (S.A.W.W)mafi kowa iya zama da jama'a ya riqa dora Abubakar kan wasu ayyuka don mu sami abin koyi.

KARANTA NAN: Sister a Social Media Fita Na Daya (1)

Misali shine, tafiyar Hijra zuwa Madinah da kuma yaqin Khaibar kafin ya tura Imam Ali (A.S).

Bangaren yara masu ilimi, fikira da sallamawa kuwa, ya riqa umartar Imam Ali (A.S)da zartar da hukunci a gabansa (S.A.W.W), kuma ya riqa tura shi yaqoqi (SARIYYA)yana jagorantar manya daga cikinsu.

Ko da a lokacin jinyarsa (S.A.W.W)ta qarshe ya umarci Sahabbansa da tafiya yaqi qarqashin Usama Bn Zaid (R.A), amma sai suka qi tafiya wai don shi yaro ne.

Abubakar ya qi tafiya, amma ya tura su Umar a qarqashinsa, shi ma Umar da yaga yarintar Usama sai ya dawo ya cewa Abubakar ya canza musu shi, ko wani comander mai yawan shekaru fiye da shi.

    (Nurul-Absar, sh:93)

IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~7th April, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post